Muna fatan sabon Gwamnan Katsina ya tabbatar da Hukumar Hisba a jihar – Rabiu Garba.

Daga RABI’U SANUSI a Kano

An yi kira ga zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr Dikko Raɗɗa, da ya taimaka wajen tabbatar da Hukumar Hisbah ta ƙasa reshen jihar dan aikin cigaban jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Wannan kira ya fito ne daga bakin sabon Shugaban Hukumar Hisbah ta jihar Katsina, Alh. Muhammad Rabiu Garba (Aminchi), jim kaɗan bayan tabbatar da shi matsayin sabon Kwamandan Hukumar na jihar.

Muhammad Rabiu Garba ya ce sahalewar Hukumar ta Hisbah a jihar zai taimaka wajen daƙile matsalolin yau da kullum da ke ƙara samun gindin za ma a wasu ɓangarorin jihar.

Don haka ya ce jihar na buƙatar makamancin aikin da hukumar ke yi a wasu jihohin dake maƙwabtaka da Katsina.

Sabon Kwamandan ya ƙara da cewa idan Allah Ya yarda za su gabatar da aikin da zai ƙara taimakon al’umma da addini a faɗin jihar da ma kasa baki ɗaya.

Haka nan, ya bayyana wasu daga cikin canje-canje da aka samu na shugabanci inda sabon Kwamandan hukumar na jihar Katsina, Muhammad Rabiu Garba ya zama Shugaban rundunar shiyyar Katsina, sai DCH Abdullahi Yusuf a matsayin Mataimakin kwamandan, ACH Muhammad Aminu Bello kuwa a matsayin sakatare da sauransu.

A ƙarshe Muhammad Garba Rabiu ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina kan su ci gaba da bai wa gwamnati haɗin kan da ya dace don ƙarfafa mata gwiwa wajen sauke nauyin da ya rataya a kanta a jihar.