HOTUNA: Atiku ya ziyarci Buhari

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, a gidansa da ke Daura yau Asabar.

Bayanan da Blueprint Manhaja ta samu ya nuna cewa, ziyarar barka sallah kamar yadda ya kai wa wasu tsofaffin shugabannin ƙasar, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalam Abubakar, kwanakin baya.