HOTUNA: Khalifah Sanusi II ya shiga Kano a karon farko bayan barin sarauta

A rana Laraba, Sarkin Kano na 14, Kalifah Muhammadu Sanusi II ya kai wa mahaifiyarsa, Hajiya Hafsat Aminu, ziyara a gidanta da ke kusa da masallacin Juma’a na Dangi a Birnin Kano.

Khalifah Sanusi yana kan hanyarsa ta zuwa Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, ne daga Legas, amma hazo ya hana shi ƙarasa wa filin jirgin sama dake Dutse, inda ya yi saukar gaggawa a Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano dake Jihar Kano.

Ziyarar tasa taƙaitacciya ce inda, bayan ya yi sallar Azahar ya hau jirgi ya koma Legas.

Majiyar Blueprint Manhaja ta ce, zai je Dutse ne, don taya sabon Sarkin Dutse, Alhaji Hameem Nuhu Sanusi, murnar ba shi sarautar, amma yanayin hazo ya kawo cikas.

Idan za a iya tunawa, Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta cire Khalifah Sanusi daga sarautar Sarkin Kano, ranar 9 ga Maris, 2020, sannan ta haramta masa shiga Kano, inda tun daga lokacin yake zaman gudun hijira a Legas. Amma daga bisani Kotun Tarayya dake Abuja ta haramta hana shi shiga Kano kuma ta ci tarar Gwamnatin Jihar Kano Naira miliyan 10 bisa tauye masa haƙƙin. Amma gwamnatin ta ɗaukaka ƙara.

Ga yadda ziyarar ta kasance cikin hotuna:

HOTUNA: Sani Maikatanga