A yi aiki da hankali wajen zaɓen shugabanni nagari

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Duk da ƙalubalen tsaro da ake cigaba da fuskanta a wasu sassan ƙasar nan da suka haɗa da matsalar hare-hare kan ƙauyawa da satar jama’a, daga yankin Arewa maso Yamma, ga cigaba da kai hare-hare kan ofisoshin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa a wasu jihohin Kudu maso Gabashin ƙasar nan, sai kuma matsala ta baya-bayan nan ta hare-hare da wasu fusatattun ‘yan Nijeriya ke kai wa kan bankuna, sakamakon halin matsi da talakawa suka shiga na rashin kuɗi a hannu don gudanar da kasuwanci da wasu harkokin rayuwa, a dalilin sauyin kuɗi da tsare-tsaren gwamnati, babu alamun za a ɗage zaɓukan da ke tafe.

Gwamnati, ‘yan siyasa da ‘yan Nijeriya na dakon zuwan lokacin gudanar da Babban Zaɓen 2023, inda za a zaɓi sabon shugaban ƙasa da zai maye gurbin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da sabbin gwamnoni a wasu jihohin Nijeriya, yayin da wasu Gwamnonin kuma ke neman tazarce don samun dama a karo na biyu. Akwai kuma zaɓen ‘yan Majalisar Ƙasa da na jihohi, da su ma za su fafata a rumfunan zaɓe, don neman amincewar talakawa, ko dai su sake komawa kan kujerunsu na wakilci, ko kuma wasu sabbin ‘yan takara su samu shiga majalisa a karon farko.

Akwai jam’iyyun siyasa 18 da za su fafata a wannan babban zaɓe da ke tafe, saɓanin 91 da aka yi wa rijista a Babban Zaɓen 2019 da ya gabata, wanda zai gudana kamar yadda aka tsara a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023. ‘Yan takarar kujerar shugaban ƙasa 18 ne, suka tsaya tare da masu mara musu baya a matsayin mataimaka da jimillar su ya kai 36. Sannan akwai ‘yan takarar kujerar majalisar ƙasa, 1168 wannan ya haɗa da ‘yan takarar kujerun Majalisar Dattijai 1100 da na Majalisar Wakilai 68.

A matakin jihohi kuma a zaɓen da za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2023, za a fafata ne a tsakanin ‘yan takarar kujerar Gwamna da ke ƙarƙashin jam’iyyu 18 da yawansu ya kai 418, idan an haɗa har da mataimakansu sun kai 837. Yayin da za a fafata tsakanin ‘yan takarar kujerar majalisun dokoki na jihohin Nijeriya su 10231, waɗanda ke neman wakiltar mazaɓu daban-daban a jihohinsu.

Lallai wannan ba ƙaramin aiki ba ne a gaban Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa wato INEC, jami’an tsaro da ‘yan Nijeriya, waɗanda za su je su shiga layi a tantance su, sannan su kaɗa ƙuri’unsu ga ‘yan takarar da suke so su wakilce su ko su shugabance su, a wannan Babban Zaɓe mai zuwa, wanda aka tsara gudanar da shi a rumfunan zaɓe dubu 176 da 846.

Sai dai abin tambaya a nan shi ne waɗanne irin mutane za mu zaɓa su zama mana wakilai ko shugabannni a matakai daban-daban? Waɗanne buƙatu muke da su gare su da muke sa ran in sun samu nasara za su yi mana, don inganta rayuwarmu da cigaban yankunan mu? Shin waɗancan shugabanni ko ‘yan majalisun da muka zava a zaɓen baya sun cika mana alƙawuran da suka yi mana lokacin da suke yaƙin neman zaɓe, da neman goyon bayan mu? Wanne darasi muka ɗauka daga irin ‘yan siyasar da a baya suka yaudare mu ko suka aikata mana abubuwan da ba a kansa muka zave su ba, suka bar mu cikin ƙunci da koma baya?

Waɗannan tambayoyi ne da ya kamata mu yi nazari a kansu, ba wai mu rufe idanun mu ko toshe kunnuwan mu daga ‘yan takarar da suka fito neman goyon bayan mu ko ƙuri’un mu ba, don kwaɗayin abin da za su ba mu, na daga kuɗaɗe ko kayan abinci, ko kuma don suna da alaƙa da wani babban mutum da muke gadara da shi, kamar wani shaihun malami ko fada ko wani basarake, ko kuma saboda addinin mu ko ƙabila mu ɗaya ba. Lokacin da za mu riƙa kallon waɗannan abubuwa a matsayin madubin mu na siyasa, ya wuce tuntuni.

Yanzu lokaci ne da ‘yan Nijeriya za su buɗe idanunsu su je rumfunan zaɓe da niyyar zaɓen ‘yan takarar da suke kyautatawa zaton za su kawo musu cigaba, kuma su samar da dokoki da tsare-tsare da za su kawo sauyi a harkokin tattalin arziki, inganta tsaro, walwala, harkar kiwon lafiya, bunƙasa ilimi, da samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasan mu da ke watangaririya babu ayyukan yi.

Mu zaɓi shugabanni masu ilimi da gogewa a kan fannonin rayuwa da shugabanci, waɗanda suka san dabarun mulki da makamar yadda za a samar da kuɗaɗen shiga da yadda za a yi aiki da su don bunƙasa ƙasa da cigaban al’umma. Kada mu sake a yi ta raina mana tunani, muna kwan gaba kwan baya, babu wani canji na musamman da talaka zai gani ya yi maraba da shi, ko a bar wa ‘yan baya su gani su san gwamnati ta yi aiki. Kamar yadda har yanzu ake tunawa da kyawawan ayyukan Marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato wanda aka samar a kowanne yanki na Arewa ba tare da wariya ko nuna bambanci ba.

A guji zaɓen tumun dare, mu tabbatar mun san wanda za mu zaɓa, kuma mun sannan manufofinsa ga cigaban mu da albarkatun da suke yankunan mu. Waɗanda suka san mu tare da matsalolin mu, kuma suka san yadda za su yi maganar maganin su.

Masu azancin magana na cewa adalin shugaban shi ne wanda yake ɗaukar shugabanci a matsayin hidima da bautawa jama’a ba, ba wanda zai riqa satar dukiyar ƙasa don raya kansa ba da iyalansa ba, ya mayar da talakawa kamar bayi.

Allah ya ba mu shugabanni nagari, masu tausayinmu da al’ummarmu.