Yadda za ku kai rahoton masu sayar da sabbin takardun Naira

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya fitar da wasu hanyoyi domin bai wa ‘ya ƙasa damar kai rahoton masu sana’ar POS da ke cajin fitar hankali idan an zo cire kuɗi.

Darakta a CBN, Mr Joseph Omayuku, shi ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da suka shirya ranar Talata a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.

Omayuku ya gargaɗi masu wannan hali da su daina, kana ya shawarci jama’a da su yi amfani da waɗannan hanyoyi na ƙasa wajen kai rahoton duk wani mai POS da aka samu yana karɓar caji wuci misali:

07002255226; Telephone Ext: 711025 – 7; [email protected] haɗi da kafofin sadarwa na zamani na CBN.

A halin da ake ciki, ƙarancin sabbin takardun Naira na ci gaba da addabar ‘yan ƙasa, yayin da da yawa sun daina karaɓar tsoffin takardun na Naira.

Lamarin da ya sa wasu gwamnoni suka ɗauki matakin maka Gwamnatin Tarayya a kotu.

An jiyo Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya faɗa a ranar Talata cewar babu buƙatar tsawaita wa’adin 10 ga Fabrairun da aka ƙayyade don daina amfani da tsofaffin takardun N200 da N500 N1,000.

Emefiele ya ɗora alhakin ƙarancin sabbin takardun Naira da ake fuskanta kan wasu ma’aikatan bankunan kasuwanci da sauran jama’a waɗanda ke ƙoƙarin hana ruwan sabbin tsare-rsaren CBN gudu yadda ya kamata.

Ya yi gargaɗin duk wanda aka kama da wannan hali za a hukunta shi daidai da doka.