Gangamin zaɓen 2023: APC ta bayyana gamsuwarta da goyon bayan al’ummar Jihar Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Yobe, Alhaji Muhammed Gadaka ya nemi haɗin kan dukkan magoya bayan Jam’iyyar APC a Yobe ta Kudu domin samun nasarar babban zaɓe mai zuwa na 2023.

Shugaban Jam’iyyar ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a yaƙin neman zaɓen da Jam’iyyar APC ta gudanar a shiyya ta biyu (Zone B), a filin wasa na Dabo Aliyu da ke ƙaramar hukumar Potiskum a Jihar Yobe.

Gadaka ya bayyana cewa, sai ta hanyar cikakken haɗin kai da goyon bayan al’ummar yankin ne Jam’iyyar APC za ta samu nasarar lashe dukkan kujerun da jam’iyyar take takara a matakai daban-daban a yankin da jihar baki ɗaya.

A nashi jawabin a wajen taron yaƙin neman zaɓen, ɗan takarar mataimakin shugaban qasa na Jam’iyyar APC Sanata Kashim Shettima, ya sadaukar da takararsa ga ɗimbin magoya bayan Jam’iyyar APC a jihar.

Sanata Shettima ya ƙara da cewa, jihar Yobe tamkar jihar da aka haife shi ce, “saboda a nan Potiskum na yi karatun sakandare, wanda haka duk nasarorin da na samu a rayuwata samu ne sakamakon abin da na samu a nan Potiskum.”

Sanata Shettima ya bayar da tabbacin cewa idan al’ummar Nijeriya suka zaɓi Tinubu/Shettima, ko shakka babu gwamnatinsu za ta magance matsalolin da suka shawo kan al’ummar ƙasar nan.

A nashi jawabi a wajen taron, Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya ce al’ummar Yobe ta Kudu sun bai wa maras da kunya kuma hakan babban qalubale ne ga ‘yan adawa, “amma za mu tabbatar da hakan ta hanyar ɗimbin ƙuri’un da za su kai jihar ga babbar nasara a zaɓe mai zuwa.

“Saboda ko shakka babu za mu tabbatar da cewa takarar Asiwaju/Shettima ta samu gagarumar nasara da quri’u masu yawa daga Jihar Yobe,” inji Lawan.

A sa’ilin da yake gabatar da nashi jawabin, Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya bayyana cewa cikakken goyon bayan da al’ammar Yobe ta Kudu suka bayar a gangamin yaƙin neman zaɓe a Potiskum, ya ƙara wa Jam’iyyar APC karsashi, qwarin gwiwa wajen samun gagarumar nasarar fiye da kowace jam’iyya.

Gwamna Buni ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga dubban magoya bayan Jam’iyyar APC a garin Potiskum, inda ya ce ko shakka babu jam’iyyar ce za ta lashe dukkan kujerun da ‘yan takararta suka tsayar; takarar Shugaban Ƙasa, Gwamna, ‘yan majalisun tarayya da na jihohi a ƙarƙashin Jam’iyyar APC.

Gwamna Buni ya ce, “dubun-dubatar magoya bayan Jam’iyyar APC a wannan shiyya ta biyu (Zone B) ya fassara mana yanayin yadda za mu samu gagarumar nasarar ƙuri’un al’ummar, wanda bisa haƙiƙa wannan babban abin alfahari ne ga ‘yan takararmu na Jam’iyyar APC,” inji Buni.