
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, tare da wasu shida bisa tuhume-tuhume guda 11 masu alaƙa da zargin rashawa, halasta kuɗaɗen haram da sauran laifuffuka masu alaƙa da badaƙalar kwangilar kyamarorin tsaro.
Sauran waɗanda ake tuhuma tare da El-Rufai sun haɗa da Jimi Lawal, da kuma kamfanonin singularitynetworksecurity.com, Solar Life Nigeria Limited, Knowledge Investment Nigeria Limited, Intercellular Nigeria Limited da Noble Coast Resources Limited.
Haka kuma, ICPC ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa Bashir El-Rufai, wanda wa ne ga El-Rufa’i ana cigaba da neman sa ruwa a jallo kasancewar shi ma yana da hannu a tuhumar.
A cewar hukumar, sababbin tuhume-tuhumen sun haɗa da zarge-zargen almundahana, karkatar da kuɗaɗen jama’a da kuma wasu laifuffuka da suka shafi gudanar da kwangilar aikin CCTV a jihar Kaduna da adadin kuɗinsa ya kai Naira biliyan 8,682,574 da aka ba kamfanin Singularity Network Security Limited.
An gurfanar su El-Rufa’in ne a gaban Mai Shari’a Hauwa’u Buhari ta Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna.
Hukumar ICPC ta yi zargin cewa an bayar da kwangilar ne ta hanyar saɓa wa dokokin mallaka da dukiyar al’umma, tana mai iƙirarin kamfanin ba shi da ƙwarewa ko cancantar aiwatar da aikin.
Ana sa ran kotu za ta cigaba da sauraron shari’ar domin tantance hujjojin da ɓangarorin biyu za su gabatar akan al’amarin.
