Daga AISHA ASAS
Kungiyar mawaƙan mata ta Koriya ta Kudu, ILLIT, ta sake shiga kasuwar kiɗa da sabon ƙaramin kundi mai suna Break Eɓen, wanda ya mayar da hankali kan yanayin soyayyar da mutum ke bayarwa amma bai samun kulawar da yake fata daga ɗayan ɓangaren.
Jaridar The Korea Times ta ruwaito cewa ƙungiyar ta fitar da kundin a ranar 26 ga Oktoba, 2026, tare da gina saƙonsa a kan fahimtar cewa wani lokaci mutum kan dage wajen nuna ƙauna, amma daga ƙarshe ya gane cewa dangantakar ba ta tafiya yadda ya tsara.
Waƙar da ke kan gaba a kundin ita ce You’re Under Arrest. An yi amfani da salon barkwanci da kalmomin da suka shafi kama mai laifi wajen bayyana takaici da fushin da kan taso idan mutum ya ji cewa shi kaɗai ne ke ƙoƙarin ciyar da dangantaka gaba.
Maimakon gabatar da wannan yanayi a matsayin labarin baƙin ciki kawai, ILLIT ta haɗa waƙa da rawa da kuma salo na kwaikwayo domin isar da saƙon cikin yanayin da zai iya jan hankalin matasa. Wannan ya ba kundin damar ɗaukar batun da mutane da dama za su iya fahimta, musamman waɗanda suka taɓa shiga dangantakar da ba ta da daidaiton kulawa.
A cewar rahoton, mambobin ƙungiyar sun bayyana cewa sun mai da hankali kan fannoni daban-daban wajen shirya sabon aikin, tun daga rikodin waƙoƙi zuwa atisayen rawa. Wannan ya nuna ƙoƙarin ƙungiyar na gabatar da wani sabon salo ga masu sauraro, tare da kiyaye abubuwan da magoya bayanta suka saba dangantawa da ita.
Kundin ya kuma ƙunshi wasu abubuwa da ke tunatar da masu bibiyar ƙungiyar daɗaɗɗun waƙoƙinta, lamarin da zai iya ba magoya baya damar ganin alaƙar da ke tsakanin ayyukanta na baya da sabon matakin da take son kai wa.
Sai dai, ba dukkan mambobin ƙungiyar ne suka shiga wannan zagayen tallata kundin ba. Moka ba ta shiga ayyukan tallata sabon kundin ba saboda hutun da take yi tun watan Yunin 2026.
Fitar da Break Eɓen ya zo ne a lokacin da ƙungiyoyin K-pop ke ci gaba da neman hanyoyin bambanta ayyukansu a kasuwar kiɗa ta duniya, ta hanyar haɗa saƙonni masu kusanci da rayuwar matasa da sabbin dabarun kiɗa, rawa da hotunan bidiyo.
