Ina kan bakana game da kalamaina kan Nijeriya – Martanin Kemi ga Shettima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Duk da sukar da mataimakin shugaban Nijeriya, Kashin Shettima ya yi mata kan zargin yin kalaman ƙasƙanci kan Nijeriya, shugabar jam’iyyar Conservatives mai ra’ayin mazan jiya a Birtaniya, Kemi Badenoch ta ce tana kan bakarta game da kalaman da ta furta a baya kan Nijeriya.

Shugabar jam’iyyar ta Conservative, wadda aka haifa a Birtaniya amma ta yi rayuwarta ta yarunta a Nijeriya, ta sha bayyana cewa ta rayu a Nijeriya ne cikin fargaba da tsoro saboda rashin tsaro a Nijeriya, wadda ta bayyana a matsayin ƙasar da rashawa ya yi wa katutu.

A ranar Litinin, mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce “idan ta ga dama za ta iya cire Kemi daga sunanta” idan ba ta “alfahari da ƙasarta ta asali”.

Lokacin da aka tambayi mai magana da yawun Kemi kan kalaman na Shettima, ya ce tana “kan bakarta a kan abubuwan da ta furta.

“Ita ce jagorar ‘yan adawa kuma tana alfahari da jagorancin da take yi na ‘yan adawa a ƙasar nan,” kamar yadda ya faɗa wa manema labarai.

“Tana faɗin gaskiya ba tare da rage komai ba. Ba za ta janye kalamanta ba.”

Lokacin wani taro kan lamarin hijira a Abuja, babban birnin Najeriya, Shettima ya ce gwamnati na “alfahari” da Badenoch “duk kuwa da ƙoƙarinta na “ƙasƙantar da ƙasarta ta asali.”

Mahalarta taron sun tafa wa Shettima a lokacin da ya ce: “Tana da ‘yancin faɗin abin da take so, tana ma da ‘yancin cire Kemi daga sunata amma wannan bai rage komai ba game da cewa Nijeriya ita ƙasar baƙar fata mafi gawurta a duniya.”

Haka nana mataiamakin shugaban na Nijeriya ya nuna bambancin da ke tsakanin yadda Badenoch ke gudanar da lamurranta da kuma na magabacinta a shugabancin jam’iyyar, Rishi Sunak wanda ɗan asalin ƙasar Indiya ne – wanda “a matsayinsa na mutum mai basira, bai taɓa ƙasƙantar da ƙasar ta asali ba”.

Babu tabbas kan takamaiman kalaman Kemi da Shettima ke magana a kai, amma dai sabuwar shugabar ta jam’iyyar Conserɓatiɓes ta sha kawo batun rayuwarta a Nijeriya cikin kalamai da jawabanta.

An haifi Olukemi Adegoke ne a Wimbledon na Birtaniya a shekarar 1980, sai dai tagirma a Legas da ke Nijeriya da kuma ƙasar Amurka inda mahaifiyarta ta yi koyarwa a jami’a.

Ta koma Birtaniya a lokacin da take da shekara 16 da haihuwa, inda ta zauna tare da wata ƙawar mahaifiyarta domin ci gaba da karatu, sanadiyyar taɓarɓarewar harkokin siyasa da na tattalin arziƙi a Nijeriya.

Bayan auren mijinta, Hamish Badenoch, wani ma’aikacin banki ɗan Scotland sai ta fara amfani da sunansa.

A taron jam’iyyar Conserɓatiɓes na wannan shekarar, Badenoch ta nuna bambancin ‘yancin da ta samu a rayuwar da take yi a Birtaniya da kuma halin da ta shiga a lokacin da take rayuwa a Legas inda ta ce “kowa a tsorace yake a kodayaushe”.

Ta bayyana birnin a matsayin wurin da babu doka, inda ta bayar da labarin yadda takan ji “ɓarayi na dukan maƙwafta a lokacin da suka je yin sata, sai ka riƙa tunanin ko gidanka za a shigo idan aka fito daga maƙwafta”.

A makon da ya gabata, lokacin da ta kai ziyara Amurka, ta bayyana birnin na Legas a matsayin “wurin da kusan komai ya lalace”.

Ta ce abubuwan da ta fuskanta a rayuwa sun sauya tunaninta zuwa tsari irin na jam’iyyar Conservatives tare da sanya ta tsanar sassaucin ra’ayi.