INEC ta gargaɗi marasa katin zaɓe kan halartar rumfunan zaɓe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta gargaɗi ’yan Najeriya da ba su da katin zaɓe, da su ƙaurace wa rumfunan zaɓe a ranar zaɓe.

Kwamishinan INEC na Ƙasa, Festus Okoye, ne ya bayyana haka a lokacin da yake karɓar kayayyakin gudanar da zaɓe a ranar Alhamis a Abuja.

Okoye wanda shi ne shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, ya ce babu wata hanyar tantancewa da za a yi amfani da su a ranar zaɓe, in ban da katin zaɓe na dindindin ba.

“Yayin da ’yan Nijeriya ke fitowa rumfunan zaɓe a ranar zave muna son nuna cewa doka ce cewa duk ɗan ƙasa da ke son kaɗa ƙuri’a a zaɓe mai zuwa dole ne ya kasance yana da katin zaɓe.

“Wajibi ne na tilas a sashi na 47 ƙaramin sashe na 1 na dokar zaɓe. Don haka mutanen da ba su da PVC ba a buƙatar su tunkari kowace rumfunan zavenmu.

“Babu wani mutum da aka yarda ya je rumfunan zaɓe ya samar da wata hanyar tantancewa banda PVC.

Ya sake jaddada cewa, INEC ta himmatu wajen yin amfani da tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a na BVAS, domin tantance masu kaɗa ƙuri’a da kuma shigar da sakamakon zaɓen zuwa manhajarta ta ‘Result Viewing Portal’ (IReV).

Okoye ya kuma tunatar da ’yan jarida da ƙungiyoyin sa ido kan zaɓe da ’yan ƙasar cewa INEC ce kaɗai ke da hurumin bayyana sakamakon zaɓen.

“Babu wata ƙungiya ta kafafen yaɗa labarai, ba wani mutum, ko ɗan ƙasa, ko wani mai sa ido a zaɓe na cikin gida ko na ƙasa da ƙasa da aka amince da shi a ƙarƙashin sharaɗi ko a ƙarƙashin doka ya bayyana sakamakon zaɓen.

“Kamar yadda wasunku suka sani, Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) shi ne Kwamishinan Zaɓe na Ƙasa baki ɗaya, kuma jami’in da zai bayyana sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa.

“Don haka shugaban hukumar ne kawai kundin tsarin mulki da kuma dokar zaɓe ya ba su damar bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

“Kowane mutum kuma hukumar za ta iya naɗa shi ya sanar da kowane matakin zaɓe,” inji shi.