Zaɓen 2023: An zo wajen!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Da gani ko da duba agogo an zo wajen gudanar da babban zaɓen Nijeriya na 2023. Duk wasu shirye-shirye na wannan zaɓe sun kammala. Ko ma dai yaya lamarin zai kasance a tsarin zaɓen Nijeriya da a kan gudanar bayan shekaru 4 ko a ce yayin da wanda ya ke kan kujera ya cika shekaru 4 kan mulki zai sauka a sanadiyyar faɗuwa zave ko kuma kammala wa’adi biyu na tsawon shekaru 8.

Shugaban Nijeriya da ke kan gado Muhammadu Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa a ranar 29 ga watan mayu mai zuwa. Don haka za a iya cewa lokacin zaɓe da a ke fatar gudanarwa lami lafiya ya zo don shirye—shiryen samun sabuwar gwamnati.

A nan mu dai za mu ce Allah ya ba wa mai rabo sa’a tun da a duk gasa a kan samu wanda zai lashe. Tsakanin ’yan takarar da su ka tsaya za a iya samun wanda zai lashe kai tsaye kamar yadda a ka saba samu tun 1999 sannan in hasashen wasu na yiwuwar gudanar da zaɓe zagaye na biyu ya afku to za a iya yin hakan.

Hukumar zaɓen dai wato INEC a taƙaice ta ce ta na shirye da bin duk yadda zaɓen ya zo na falam ɗaya ne ko zuwa zagaye na biyun. Duk wanda Allah ya raya zuwa lokacin zai ga abun da zai faru kuma mu na fatan mu ga alheri don amfanin mu ’yan Nijeriya da ke raye yanzu, yara da ke tasowa da kuma masu zuwa nan gaba.

Don ma tabbatar da shiryawa tsaf don mika ragamar mulki shugaba Muhammadu Buhari tuni ya kafa kwamitin miqa ragama ga sabuwar gwamnati ƙarƙashin sakataren gwamnatin Boss Mustapha. Aa zahiri za a iya cewa an yi saurin kafa kwamitin amma a baɗini ba haka ba ne don akwai gujewa fafa gora ranar tafiya. Hakanan gwamnatin ba neman tazarce ta ke yi ba shirin barin mulki ta ke yi don ƙarewar wa’adi.

Wani abu mai ɗaukar hankali shi ne shugaba Buhari kan ce zai miƙa ragama ga duk wanda ’yan Nijeriya su ka zaɓa. Akwai yanayi biyu a nan na tsarin shugabanci. Shi dai shugaban ƙasa kan yi magana a lokacin da ya ke magana ga dukkan ’yan ƙasa cewa zai tabbatar na yi zaɓe mai adalici kuma duk wanda ya samu nasara za a miƙa ma sa ragama.

Sai kuma a lokacin da ya hau dandalin siyasar jam’iyyar sa ya kan nuna a zaɓi jam’iyyar sa da yin fata za ta lashe zave. Abun da za mu ƙara dubawa a nan shi ne daga dawowa sabuwar dimokuraɗiyyar shekaru 24 da su ka wuce, tsohon shugaba Obasanjo ne ya kammala wa’adin sa na shekaru 8 har ma ya yi yunƙurin zarcewa a karo na 3 a 2007. Sai kuma wannan karo da shugaba Buhari ke cika shekaru 8.

Marigayi shugaba Umaru ’Yar’adua ya yi shekaru 2 ne kacal Allah ya karbi abun sa sai tsohon shugaba Jonathan da ya kammala wa’adin shugaba ’Yar’adua ya tsaya zave ya yi shekaru 4 a daidai lokacin neman tazarce ya faɗi zaɓe a 2015.

A irin wannan lokaci a zaɓen 2007 shugaba Obasanjo ya zaiyana zaɓen da cewa na ko a mutu ko a yi rai ne. Kuma gaskiya ko da a ce ba a mutu ba an samu cikas a tsarin zaɓen da a ka tabbatar hukumar zaɓe ta sanar da sakamako gabanin kammala tattara sakamakon.

Kuma wani abu mai ban sha’awa marigayi shugaba Umaru ’Yar’adua ya soki zaɓen da ya kawo shi kan gado da cewa an samu matsaloli a zaɓen. Duk da nasara a kotu marigayi shugaban ya kafa kwamitin gyara lamuran zaɓe ƙarƙashin mai shari’a Muhammad Lawal Uwais.

Shin zaɓen ya gyaru ko bai gyarau ba an cigaba da gudanar da zavuka a 2011, 2015, 2019 da kuma yanzu da mu ka zo na 2023. Gaskiya shugaba Buhari bai yi amfani da kalmar da ta yi kama da ko a mutu ko a yi rai ba. Hakanan bai zake da lalle sai an zaɓi dan takarar jam’iyyarsa ba.

Ba mamaki hakan ne ma ya kawo zargin ko ma bai damu da lalle sai ɗan takarar Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaɓen ba. Duk da haka an ga shugaban a wajajen kamfen ɗin ɗan takarar har zuwa rufewa a Legas.

Ɗan takarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya yi gangamin kammala kamfen ɗin sa a Legas da samun halatar shugaba Buhari.

Wannan dai bisa al’ada rufe kamfen ne a gida daga nan sai a jira ranar zaɓe don ganin yadda sakamako zai kaya. A wajen gangamin a filin wasa na Teslim Balogun, shugaba Buhari ya daga hannun Bola Tinubu ya na mai buƙatar a kaɗa masa ƙuri’a. A jawabinsa Tinuubu ya yi alƙawarin yi wa Nijeriya hidima in dai an zaɓe shi ya na mai yabawa shugaba Buhari don mara masa baya da ya yi.

Taron na Tinubu ya zo ne bayan kammala na ɗan takarar PDP Atiku Abubakar a Yola jihar Adamawa inda shi ma ya yi alwashin kawo cigaba a Nijeriya matuƙar a ka kada masa ƙuri’a. Ba lalle ba ne sai ɗan takara ya zo jiharsa ta asali ya rufe kamfen, amma hakan ƙara ce ga na gida.

Duk sharhin masana kimiyyar siyasa na nuna ‘yan takara 4 sun fi tasiri inda Atiku a PDP da Tinubu a APC ke sahun farko in an yi la’akari da duk jam’iyyun biyu sun riqe gwamnatin tarayya. Sai kuma a ɗaya sahun Peter Obi na Leba da Rabi’u Kwankwaso na NNPP. A gaskiya ni ban ma ga zaɓen da ba a ma sa hasashe kai tsaye irin wannan na 2023.

In ka ɗebe magoya bayan ’yan siyasa da ke cika baki cewa kafin 12 na rana sun lashe zaɓe, masu adalcin magana da ba su da gefe kan yi takatsantsan wajen bayanai inda su ke nuna zaven zai iya ba da mamaki ko abin da ma ba a yi tsammani ba shi zai faru. ’Yan takara dai sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya na zave wato in an bayyana sakamako za su amince ko da ba su lashe ba, ba tare da zuga magoya baya a tada fitina ba.

Hukumar kula da matasa masu yiwa ƙasa hidima ta Nijeriya NYSC ta ce fiye da matasan 200,000 ne a ka tura don kula da lamuran zaɓe a matsayin ma’aikatan hukumar zaɓe na wucin gadi.

Shugaban hukumar Burgediya Janar Yushau Ahmed ya biyyna hakan a taron manema labaru kan matasan da a kan tura sassan Nijeriya don kula da gudanar da zaɓe ta hanyar sarrafa na’urori.

Birgediya Janar Ahmed ya hori matasan da sam kar su yarda da duk wani yanayin da wani ɗan siyasa zai ba su wani ihsani kamar abinci da sauran su da hakan zai iya sa su sava ƙa’idar aiki ko neman fifita wani kan wani.

A nan hukumar ta ce duk matasan su tafi da guzurin da zai taimaka mu su wajen gudanar da aikin cikin natsuwa ba tare da karvar komai daga wajen wani ba.

NYSC ta ce hukumar zaɓen INEC a taƙaice ta yi alƙawarin tabbatar ɗaukar nauyin walwala da jin daɗin matasan. Idan har hukumar zaɓe za ta ba wa matasan duk walwalar da su ke buƙata don zaɓen to za a yi tsammanin su kuma za su tsaya tsayin daka wajen aiki ba ha’inci.

Cikin ikon Allah tun zaɓen 2011 da a ka samu rikicin zargin murde zave har wasu daga matasan su ka rasa ran su, ba a sake samun fitinar ba, kuma a na fata hakan zai ɗore har ma sauran zaɓuka ba adadi nan gaba.

An samu labarin hukumar zaɓen ta samu kuɗin gudanar da aikin da ta buƙaci wasu kuɗin a takarda don biyan musamman ma waɗanda za su yi sufurin kayan zaɓe a mota. Wannan ƙalubale na canjin kuɗi zai iya kawo sauyi na ko an shirya ko ba a shiya ba don na ji ’yan siyasa da ma masu amfana a irin wannan lokaci da kyautar ’yan siyasa na ƙorafi. Sarkin Kano na 14 Sunusi Lamido Sunusi ya buƙaci talakawa su mara baya ga canjin Naira ko taƙaita amfani da kuɗi da ke gudana a halin yanzu.

Sunusi Lamido wanda tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN ne, ya ce, shirin ba sabo ba ne don ya fi shekaru 10 da ƙirƙirowa. Don haka Lamido Sunusi ya ja hankalin talakawa da cewa kar su bari su fada tarkon farfagandar ’yan siyasa da canjin ya maida maƙudan kuɗin da su ka wawure tamkar ya yi.

Tsohon gwamnan bankin ya fito karara ya ce canjin ya fi shafar masu wawura da yadda ya ke shafar masu ƙaramin ƙarfi.

Kammalawa;

Ƙuri’a dai matuƙar za ta yi aiki, to za ta samarwa masu rinjaye sakamakon wanda su ka zaɓa. Ƙalubalen shi ne ya zama wanda a ka zavan bai cika alƙawari ko bai aikata abun da waɗanda su ka zaɓe shi su ka yi tsammanin zai aikata ba.

A bisa ga haka masu zaɓe su ƙara dogon nazari kafin kaɗa ƙuri’a su kuma yi addu’ar Allah ya nuna mu su gidan ’yar ta kamar a wasan nan na gargajiya ‘MALAM NA BAKIN KOGI’.