‘Yan sanda sun cafke gomman ‘yan daban siyasa a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano

A tsaka da shawartar shugabanin jami’iyyu daban daban a Jihar Kano wajen tausar su game da ƙudurin fitowar neman goyon bayan jama’a daga masoyansu da sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Muhmmad Yakubu ya gana da su.

Kamar yadda aka sani a ranar Alhamis ne 23 ga wannan watan dokar yakin neman zaɓe ta haramta ci gaba da yawon neman goyon baya ga duk wani ɗan siyasa, wanda a Kano ma haka abin yake daga ranar babu wanda zai ƙara fitowa a rana ta gaba kenan.

Duk da haka wasu daga cikin jam’iyyu ba su bi wannan umarni ba, wanda ya ba magoya bayansu damar fitowa cikin birnin na Kano tare da nuna goyon bayansu, hakan ya ba wasu daga cikin ‘yan daba fitowa domin muzguna wa al’umma wanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Cikin salon iya aiki shi kuma Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammad Yakubu ya samu bayannan sirri cewa wasu na shirin ta da zaune tsaye da muggan makamai a cikin garin wanda babu ɓata lokaci ya umarci wakilansa ɗaukar matakin da ya dace.

Nan take aka tashi jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro dake jihar da ya ba su nasarar kama aƙalla mutum 85 da aka tabbatar magoya bayan jam’iyyu daban-daban ne tare da mugan makamai kamar yadda sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya fitar wadda aka raba wa manema labarai.

Da wannan ne Kwamishinan ya jaddada buƙatar cikakken goyon baya ga jami’an tsaro daga al’ummar jihar, kana ya jinjina wa mutanen Kano baki ɗaya dangane da haɗin kan da ake ba jami’an tsaro a jihar.