Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Asabar ne jagororin Isra’ila suka amince da yarjejeniyar Gaza ta tsagaita wuta da kuma sako fursunonin da aka tsare, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin Firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu ta bayyana, wadda ake fatan ta fara aiki nan take.

A ranar Lahadi ne ake sa ran tabbatar da tsagaita wutar, wadda za ta bada damar tsayar da kai farmaki da tayar da boma-bomai a tsakanin ƙasashen biyu.

Sannan za ta bada damar sako fursunonin yaƙi da Hamas ta kama a lokacin da ta kai wani farmaki a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, a musayar fursunonin ƴan Palestine da ke tsare a gidajen yarin Isra’ila.

Ma’aikatar Shari’a ta Isra’ila ta ce za a sako fursunoni 737 kafin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Lahadi a matsayin gaɓar farko ta yarjejeniyar.

Hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza bayan sanar da tsagaita wutar sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a wurare 50.

Yarjejeniyar za ta fara aiki ne a daren rantsar da Shugaba Doald Trump na Amurka, wanda ya jagoranci samar da ita da haɗin-gwiwar Shugaba Joe Biden mai barin gado.

Haka ma Shugaban ƙasar Palestine, Mahmud Abbas ya ce hukumar ƙasar ta shirya tsaf don cigaba da gudanar da harkokin mulki a Gaza bayan kammala yaƙin.

Tuni dai mutanen Gaza suka fara shirin koma wa gidajensu gabannin ƙulla yarjejeniyar.