Shettima ya jajenta wa iyalan sojojin da suka rasa rai a Maiduguri

Daga USMAN KAROFI

Mataimakin shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, a ranar Juma’a ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu sakamakon harin ‘yan ta’adda a Damboa, Jihar Borno. Duk da haka, sojojin sun yi nasarar daƙile harin kafin rasuwarsu.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhinin sa kan wannan mummunan lamarin tare da umarnin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin harin. Ya kuma jinjina wa sadaukarwar sojojin da suka rasa rayukansu tare da yaba wa rundunar sojin saman Najeriya bisa martanin gaggawa da suka yi na kai farmaki mai nasara kan ‘yan ta’addan.

A yayin ziyarar, nataimakin shugaban Ƙasa ya kuma ziyarci gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno a madadin Shugaban Ƙasa.

Tawagar Shettima ta haɗa da Sanata Kaka Lawan, Malam Abdulkadir Rahis, Hon. Usman Zannah, ministan sufuri Sanata Saidu Alƙali, da wasu fitattun mutane kamar Malam AjiKolo Gujja.