Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Asabar ne Shugaban ƙungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) kuma Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq ya ziyarci wajen da wata tankar man fetur ta kama da wuta tare da tarwatsewa a jihar Neja.
Gwamna AbdulRazaq ya bayyana al’amarin a matsayin abin tashin hankali da tausayi ga waɗanda iftila’in ya shafa.
A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar, shugaban gwamnonin ya bayyana kaɗuwarsa ga adadin mutanen da suka rasa rayukansu da waɗanda samu raunuka da a cikin su har da waɗanda suka kai ɗauki.
Sanarwar ta ce NGF ta bayyana alhininta game da lamarin tare da miƙa saƙon ta’aziyya ga Gwamna Umar Bago da iyalan waɗanda iftila’in ya shafa.
NGF ta kuma yi kira a ga takwarorinsu da su ƙarfafa matakan kariya ga rayukan al’umma musamman a lokacin da aka samu tsiyayewar fetur.
Kazalika, ƙungiyar ta yi addu’ar fatan samun rahama ga mutanen da suka rasa rayukan nasu a yayin aukuwar lamarin.