Iyalan ɗalibin sekandiren NAF da aka kashe sun buƙaci a yi adalci

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Iyalai da wakilan cocin wani mataimakin shugaban daliban makarantar sekandire ta rundunar sojin sama (NAF) da ke Kaduna, Felix Blaise da aka kashe, sun buƙaci hukuma da ta yi adalci yayin binciken kisan

Ɗalibin mai shekaru 15, ɗan aji biyar, ana zargin an kashe shi ne a ɗakin kwanan ɗalibai inda wata jarida ta yanar gizo ta ce wasu ɗalibai su biyu ƴan aji shida ne suka sa masa lantarki wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

NAF ta ce, tana cigaba da bincike kan lamarin domin gano haƙikanin abun da ya faru.

Haka nan, wakilin cocin mamacin na ‘Lux Terra Chaplaincy’ da ke Abuja, ya ce wasu ɗalibai biyu ne ƴan aji shida da ba’a san ko su waye ba ne suka kashe Felix ta hanyar lantarke shi.

Wani kawun mamacin mai suna Paul, ya ce Felix yaro ne wanda ya rasa mahaifansa a shekarar 2013, sannan kuma ya ziyarce shi a makarantar a lokacin hutun sallah inda ya ce ya same shi lafiya lau.

Paul yayi kira ga hukumar makarantar da NAF, da su karrama mamacin ta hanyar gano makasan nasa.

Ya ƙara da cewa “muna da tabbatacin ana cigaba da gudanar da bincike kan kisan ɗanmu kuma hukumar makarantar da NAF amintattu ne a wajen mu, don haka muke fatan su yi adalci” inji shi.

Leave a Reply