Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano
Ƙungiyar Jama’atu Izatul Bid’a wa Iƙamatus Sunnah mai helkwata a garin Jos, wadda kuma Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ke jagoranta, ta buɗe gidauniyar neman taimakon kuɗi Naira miliyan 30 a Kano don gudanar da ayyukan ƙungiyar.
Shugaban Majalisar Malamai na Izalar Jos, Sheik Sani Sharif Umar Bichi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi wurin taron ƙaddamar da gidauniyar neman taimakon kuɗin don taimakon addinin Musulunci wanda ya haɗa da samar da hedikwatar ƙungiyar mai haɗe da masallaci da makaranta a Kano. Sai kuma ciyarwa da hidimar tafsirin azumin Ramadan don faɗakar da jama’a.
- Haɗarin shigar da addini cikin siyasa
- Muhimmancin aure a addinin Musulunci da rawar da iyaye za su taka akan tarbiyyar yara (2)
Sheikh Sani Sherif ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen gudanar da ayyukan ƙungiyar da suka haɗa da ɗaukar nauyin karatuttuka da wa`azozi a kafafen yaɗa labarai da sauran ayyukan ƙungiya kamar shirya taron ƙara wa juna sani, musabaƙa da ilimantar da mahajjata da kuma samar da ƙarin motocin ƙungiyar don cigaba da ayyukan ƙungiya.
Shi ma shugaban gudanarwa na ƙungiyar, Alhaji Muhammad Sadi Yahaya ya ce JIBWIS mai shalkwata a Jos an kafa ta ne domin wa’azantar da al’umma ingantacen tauhidi da zai rabasu da abubuwa marasa kyau wanda shari’a ta hana kamar shirka, bidi’a camfi da aauran su.
Saboda haka ya yaba wa waɗanda suka bada tallafi na kuɗi da addu’a da goyan baya ga ƙungiyar da sauran jami’an gwamnatin Kano da waɗanda suka taimaka.
Taron dai ya samu halartar malaman ƙungiyar da dama kamar su Malam Khamisu Unguwa Uku; ɗaya daga cikin limamai kuma masu faɗakarwa a ƙungiyar sai kuma Malam Ismail Abubakar Jega babban kwamandan agaji na Izala.
