Haɗarin shigar da addini cikin siyasa

Manhaja logo

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A ƙarshen makon da ya gabata ne wata sabuwar muhawara ta kunno kai a cigaba da shirye shiryen Babban Zaɓen 2023, bayan wani rubutu da wani fitaccen malamin Jami’a da ke zaune a ƙasar Amurka, wanda ya yi fice wajen rubuce-rubuce a shafukan jaridun Nijeriya game da batutuwan da suka shafi ilimi, siyasa da zamantakewa a ƙasar nan, wato Farfesa Farouq Kperogi, ya yi. 

Shi dama wannan marubuci ba ɓoyayye ba ne wajen rubuce-rubuce masu rikitarwa da sanya ruɗani, wanda wasu ke yi masa kallon ɗan adawar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ko kuma ɗan koren Yahudawa, saboda yadda rubutun sa ke karo da akasarin ra’ayoyin al’ummar Arewa, duk kuwa da kasancewar sa Musulmi daga Arewa.

Rubutun sa na baya-bayan nan ya yi ne kan wasu hujjoji goma da ya tattara kuma ya ke ganin sun isa su tabbatar da zargin da yake yi wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin mai tsananin kishin ra’ayin Kiristanci wanda kuma yake siyasa don kare muradun addininsa. Rubutun da ya yi ya biyo bayan fitar sanarwar shiga takarar neman shugabancin ƙasar nan da Mataimakin Shugaban Ƙasa ya yi, wanda kuma aka ce har ya sanar da shugaban ƙasa.

Wannan ne ya sa wasu ‘yan Nijeriya ke zargin an fitar da rubutun Farfesa Kperogi ne don a vata sunan Mataimakin Shugaban Ƙasa da takarar da yake so ya yi. Sai dai kuma wasu bayanai da ke ƙara fitowa a kafafen watsa labarai na ƙara tabbatar da akwai ƙamshin gaskiya a rubutun Farfesa Kperogi.

A wani rubutu da mawallafin mujallar Ovation Dele Momodu ya fitar a jaridar Punch, ɗan jaridar ya bayyana ra’ayin sa game da matakin da Majami’ar Redeemed Christian Church of God (RCCG) ta fitaccen mai wa’azin Kiristan nan Pastor Enoch Adeboye, ta ɗauka na buɗe Sashin Kula da Harkokin Siyasa da Shugabanci a ƙarƙashin kulawar majami’ar, inda ya yi zargin cewa an buɗe sashin ne domin yaɗa manufofin siyasa da mara wa takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa baya, bisa la’akari da cewa majami’ar waje ne na addini, zargin da majami’ar RCCG ta musanta. 

Momodu ya bayyana cewa, abin da RCCG ke ƙoƙarin yi, idan zargin sa ya tabbata, babban haɗari ne ga zaman lafiyar Nijeriya, kuma kuskure ne mai girma. Ya ƙara da cewa, “na yi imanin cewa shugabannin wannan majami’a sun yi aiki tuƙuru don ganin kafuwar wannan majami’a da ta shahara a duniya. Ban ga wani abu da zai kawo wa wannan majami’a ruɗani ba. Amma sanya addini a cikin siyasa babban haɗari ne ga Nijeriya a yau. Kamar dai haɗa wasu manyan sinadarai ne masu sanya wuta a ɗakin binciken kimiyya. Ba wai kawai sakamakon hakan zai zama mai illa ba ne, zai iya zama mummunan al’amari da zai buwayi kowa da kowa a ƙasar nan. Allah ya kiyaye.”

Ya kuma shawarci shugabannin majami’ar da su yi hattara wajen ɗaukar wannan mataki, domin kuwa Mataimakin Shugaban Ƙasa ba shi kaɗai ne ɗan siyasa da ke zawarcin neman kujerar shugaban ƙasa a cikin majami’ar ba, wanda hakan na iya haddasa ruɗani da rabuwar kai, duba da kasancewar Sanata Remi Tinubu mai ɗakin Sanata Ahmad Bola Tinubu mamba ce mai muhimmanci a RCCG, duk kuwa da kasancewar mijinta tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma ɗaya daga cikin masu neman takarar shugabancin ƙasar nan, Musulmi ne. 

“Shawarata a nan ita ce majami’un mu su kawar da kai daga wannan batun baki ɗaya, domin kaucewa sake jefa ƙasar nan cikin wani sabon rikicin addini da ya daɗe yana cutar da ƙasar nan. Yaya ku ke tsammani idan sauran majami’u ko wasu addinan suka fara bayyana aniyarsu ta goyon bayan mabiyin addinin su ko aƙidarsu kaɗai. Wannan ba zai taɓa zama alheri ga ƙasar nan ba. Nijeriya za ta fuskanci matsala mai girma da za ta haifar da cece kuce da fitintinu iri-iri.”

Wannan ita ce babbar shawarar da duk wani ɗan Nijeriya mai aiki da hankali zai bai wa malaman addini a ƙasar nan, matuƙar ana son ganin an gudanar da Babban Zaɓe mai zuwa na 2023 cikin lumana da kwanciyar hankali. Amma abu ne mawuyaci a raba ɗan Nijeriya da batun addini da siyasa, musamman idan aka yi la’akari da abubuwan da suka faru a lokacin takarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, zaɓen da ya kai shi ga wannan babbar kujera da ya daɗe yana nema. 

Idan ba za mu manta ba, tun a wancan lokacin haka aka yi ta yaɗa jita jita da rubuce-rubucen cewa, idan har kiristan Nijeriya suka bari Buhari ya zama shugaban ƙasa to, sai ya musuluntar da ƙasar nan, ta hanyar sanya dokoki da tsare-tsare da za su ƙuntatawa sauran waɗanda ba Musulmi ba. Kuma wannan zargi ya yi tasiri sosai a zukatan wasu ‘yan Nijeriya, ta yadda tilas ta sa shugabannin Jam’iyyar APC a lokacin Babban Zaɓen 2011 suka yanke shawarar fitar da Farfesa Yemi Osinbajo fitaccen mai wa’azin Kirista, don ya yi masa mataimaki. Wannan mataki ya taimaka wajen kashe waccan wutar da ta kunno kai a lokacin. 

Sake dawo da wannan tsohon salo na kawar da hankalin ‘yan Nijeriya da sanya fargaba da ruɗani a ƙasar nan babban abin takaici ne, da ya kamata duk wani ɗan Nijeriya mai son zaman lafiya da cigaba ya ƙyamata, kuma ya nesanta kansa da shi. 

Daga ɓangaren Musulmi da Kirista duka akwai wannan matsala, kowanne ɓangare yana ɗaukar samun madafun iko da ƙarfin faɗa a ji a siyasance, wani makami ne a wajen sa na yi wa addininsa hidima, kuma yana sa ran samun lada mai girma a wajen Ubangiji. Malamai a masallatai da minbarorin wa’azi, da faɗa-faɗa da ke jagorantar mabiya a majami’u, a duk lokacin da kakar siyasa ta kama sukan shagala wajen kira ga mabiyan su da  almajirai zuwa ga kiraye kirayen a zaɓi ɗan takarar da yake Musulmi ko Ƙirista, ko wanda ya ke yi wa addini hidima, don suna ganin shi ne aikin da Allah zai yi farin ciki da shi. 

Rahotanni na ci gaba da kawo labarai game da wa’azozin malamai, daga ɓangaren Musulmi da Kirista, da ke kira ga mabiyan su su je su yi rijistar katin zaɓe, su mallaki shaidar jefa ƙuri’arsu a hannu, don su yi wa addini aiki da ita. Su zavi ɗan uwan su da zai kare musu addininsu! Kai ka ce raba ƙasar za a yi ta fuskar addini, ba siyasa ba ce. Kaico!! 

Alhalin su ‘yan siyasar a nasu ɓangaren sun san cewa suna yi ne don cimma burin su na samun iko da hawa kujerar mulki, ba don yi wa addini aiki ko don kishin addinin su ba. Amma addini shi ne ya zama babban makamin da suke da shi na raba kan jama’a da jawo musu goyon baya sosai, abin da zai ba su damar samun abin da suke so a sauƙaƙe. Ko da kuwa a zahiri sun nuna kansu a matsayin na Allah ne ko kuma kishin addini ne ya sa suke siyasa. 

Amfani da siyasa don samun sauqin samun nasara da goyon baya ragwanci ne da rainin hankali, kuma yaudara ce da cin amanar talakawa. Siyasa harka ce ta neman mulki don sarrafa madafun iko, da arzikin ƙasa. Ko da Musulmi ne ko Kirista ya samu nasara abin da ake buƙata a wajen sa shi ne adalci da riƙon amana. Addininsa zai amfani jama’a ne kaɗai idan ya yi biyayya ga rantsuwar da ya yi ta kama aiki, kuma ya tsarkake zuciyar sa daga yaudara da nuna bambanci a tsakanin jama’ar da ya ke mulka. 

A irin yanayin da Nijeriya ta ke ciki na rashin ingantaccen tsaro da rashin yarda da juna a tsakanin ƙabilun ƙasar nan, yaɗuwar ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da ke fafutukar ɓallewa daga Nijeriya, da tsadar rayuwa, ba daidai ba ne a wannan lokaci a shigo da batun goyon bayan ɗan takarar da ya fito daga wannan addini ko wancan, ko daga wannan ɓangaren qasa zuwa waccan. Abin mayar da hankali shi ne waɗanne manufofi ya zo da su da za su fitar da Nijeriya daga halin da ta ke ciki, kuma ya kawo sauyin da zai kyautata rayuwar kowanne ɗan ƙasa. 

Babu wani lada da za mu samu daga zaɓen azzalumin ɗan siyasa, mayaudari, ko maƙaryaci, don kawai ya kasance Musulmi ko Kirista. Kuma babu wani ɗan siyasa don kawai yana sallah ko yana zuwa coci da zai yi amfani da damar da ya samu ta mulki wajen canja addinin wani ko hana wasu ‘yancin su na yin addinin da suka zaɓa wa kansu. Ya kamata malamai da masu wa’azi da ‘yan siyasa su ji tsoron Allah, su daina yaudarar jama’a, kuma su daina haddasa fitina a ƙasa don kwaɗayin abin duniya. 

Abin takaici ne yadda Nijeriya ta zama ƙasa mai yawan mabiya addinai da kishin yin ayyukan ibada, amma kuma aka mayar da addinin ya zama abin wasa, makamin faɗa da juna da yaudara. 

Siyasar addini ba alheri ba ce ga siyasar ƙasar nan Nijeriya! Mu yi hattara. Allah ya ba mu shugabanni nagari masu tausayin talakawa da riƙon amana daga kowanne addini suke, matuƙar za su yi wa ‘yan Nijeriya adalci. Wannan shi ne abin talakawan ƙasar nan ke nema.