Jakadan Ƙasar Sin a Najeriya ya ziyarci Lagos

Daga CMG Hausa

Daga ranar 7 zuwa 9 ga watan nan, jakadan ƙasar Sin a Tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya ziyarci jihar Lagos, inda ya gana da gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu.

Yayin ganawar tasu, Cui Jianchun ya ce, jihar Lagos tana kan gaba a Najeriya a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da kasuwanci da masana’antu, kuma wuri ne da baƙi Sinawa suka fara zuwa a Najeriya domin yin ciniki da kasuwanci a ƙasar.

Ya ce yankin yin ciniki cikin ‘yanci na Lekki, da masana’antar tace mai ta Dangote, da aikin tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki, waɗanda kamfanoni masu jarin ƙasar Sin suka kafa suna cikin jihar ta Lagos, waɗanda suke taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar haɗin gwiwar da ke tsakanin ƙasashen 2.

Kazalika ƙasar Sin na son zurfafa haɗin gwiwa a tsakaninta da jihar Lagos a sassa daban daban, musamman ma manyan ababen more rayuwa, da aikin sadarwa, masana’antu, zuba jari da cinikayya, ƙarƙashin tsarin manyan tsare-tsaren samun ci gaba da bunƙasa na 5GIST tsakanin Sin da Najeriya.

A nasa ɓangaren, gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce, yankin ciniki cikin ‘yanci na Lekki yana bunƙasa yadda ya kamata. Kuma ana dab da kammala kafa masana’antar tace mai ta Ɗangote, da aikin tashar jiragen ruwa mai zurfi ta Lekki.

Ƙasar Sin ta bai wa jiharsa babban taimako a fannin samar da manyan ababen more rayuwa.

Ya ce duk irin sakamakon da za a samu a babban zaɓen ƙasar a shekara mai zuwa, jihar ta Lagos za ta ci gaba da haɗa kai da ƙasar Sin, a ƙoƙarin ƙara azama kan aiwatar da ƙarin ayyukan da za su amfani al’umma.

Fassarawar Tasallah Yuan