Dandalin shawara

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA: Salam. Asas barkan mu. Don Allah ni matsalar da na ke da irin kin gane ba Ina da suruka irin munafukan tsofaffin nan. A gaban mijina sai ta nuna tana so na amma idan ba idonshi sai ta yi ta cin zarafi na, ta yi ta kai ƙara na. Na yi ƙoƙarin fahimtar da shi amma kuma sai dai mu yi ta faɗa. Ki taimaka min da shawarar yadda zan kawo ƙarshen lamarin.

AMSA: Da farko dai dole sai kin fara da canza irin kallon da kike yi wa uwar mijin taki matuƙar kina so ki samu mafita kan lamarin. Kalmar ‘munafukan tsofaffi’ da kika danganta ta da ita ma zata iya fassara matsayinta a baki da zuciyarki. Ban sani ba ko hakan ya samo asali ne da irin ababen da ta ke ma ki na rashin kyautawa har mutuncinta ya zube a idonki, ko kuwa tun farko kallon da kike yi mata kenan.

Koma dai menene, bata cancanci ki dinga yi mata irin wannan suna na rashin kyauta wa ba, duk da cewa ta taka wannan sunan a zamantakewar ku. Ki kwantata da uwar cikinki, matuƙar kina son ki samu zaman lafiya a zamantakewarku.

Idan mahaifiyarki na ma ki ba daidai ba, me kike yi? Ina ce haƙuri tare da nemo hanyar da za ki kawo ƙarshen fushin nata cikin ruwan sanyi. To shi ma haka yake fatan ki yi ga mahaifiyarshi, kamar yadda yake yi shi ma.

Wani kuskure da mata ke yi lokuta da dama shine, ƙoƙarin daidaita matsayinsu da na uwar mijinsu, ko kuma dagewa sai mijin ya ba wa uwar tasa rashin gaskiya a lokacin da ta yi masu ba daidai ba. Wannan kuwa na ɗaya daga cikin dalilan da ke rura wutar fitina a tsakanin ma’aurata.

Domin shi ba zai iya ba wa mahaifiyarsa laifi ba koda kuwa ya san tana da shi, ba don komai ba, sai don tana uwa gare shi, don haka ba shi da zaɓi face bata haƙuri ko a yanayin rashin gaskiyar ta. Ke kuwa da yake da iko sai ya ba ki rashin gaskiyar. Wanda ya kamace shi da ya ba ki haƙuri yayin da kuka keɓe.

Idan mun juya ga matsalarki, zan iya cewa, akwai hanya mai sauƙi da za ki iya magance matsalar, amma fa mai wahalar ɗauka ga zuciyar da bata da haƙuri. Ita ce amsar duk wani laifi da ta faɗa na ki. Ma’ana dai ke ma ki shiga wasan kwaikwayon da ta ke shiryawa. Ta hanyar zama jarumar shirin, duk yadda ta rubuta labarin ya zama daidai a wurinki.

Na san za ki ce ta ya hakan zai ba ni mafita? Idan kin duba matsalar dukka dai burin nata shine sanya fita da rashin zaman lafiya tsakanin ki da mijinki, to kuma ‘matar na tuba aka ce bata laifi’. Duk lokacin da ta ya kawo ƙarar kin mata ba daidai ba, yi sauri ki bata haƙuri tare da nuna kin karɓi kuskurenki, ba tare da ja ko musu ba, to me zai biyo baya?

Dole duk faɗan da zata yi haƙurin dai zata yi, shi kuma kin kashe wutar fitina tsakanin ku, domin ko zai yi faɗa na ɗan lokaci ne tunda kin karɓi laifin. Kuma akwai hanyoyin da mata ke bi da taimakon kissa wurin hana miji jan faɗa da nisa ko fushi mai tsayi, kinga ta wannan hanyar ma za ki iya daƙile kawo ƙarar da ta ke yi. Domin idan ta ga bata samun yadda take so, dole ta juya wani ɓangaren.

Abu na biyu da za ki iya samu albarkacin amsa laifin shine, yardar mijinki, wadda zata zo bayan dogon tunanin da mijin na ki zai yi, don an ce, idan mafaɗi bai da hankali, shi fa majiyi. Zai ga a kullum tana kawo ƙarar ki, kuma kina amsa laifin ba gardama, kuma ke bai ji kin kawo masa ƙara ko ɗaya ba. A nan zai saka ayar tambaya. A hankali za ta fara kawo ƙarar abinda ya tabbatar ba halinki ba ne, sai ya fara kokwanto kan gaskiyar maganar tata. To a lokacin ne zai fara sha’awar jin gaskiyar zance daga bakinki, koda kuwa idan kun keɓe ne. A nan za ki samu damar wanke kanki ba tare da tashin hankali ba.

Kinga sai ki mayar da ita mahaukaciya a ganinta, domin za ki amsa laifin ne a gabanta, yayin da mijinki zai rarashe ki a bayan ta. Idan kuwa ta fara canza kala a lokacin da ba ya kusa, sai ke kuma ki koma kurma, wadda bata jin sautin muryarta, ta hanyar bin ta da ido kan duk irin maganganun da zata yi ma ki.

Akwai hanyoyi da yawa da za ki iya hana tasirin maganganunta a zuciyarki. Kuma da matakin farko zan iya cewa, za ki kai lokacin da ko yi mata kika yi ba zai yarda ba.(sai dai ba Ina ba ki shawarar yi mata rashin mutunci ba, saboda ciki mai gaskiya ne kawai wuƙa bata iya fasawa. Kuma ɗaya idan kika yi ya gane, kin rusa yardar da kika jima kina gina wa a tsakanin ku.)

Daga ƙarshe zan ba ki shawarar ki kasance a jerin matan da ke taimaka wa mazajensu ta hanyar neman lahirar su, ta hanyar taya shi neman yardar mahaifiyarshi.

Ku aiko da tambayoyinku ta [email protected] ko [email protected]