Daga AISHA ASAS
Shafin kwalliya na satin da ya gabata ya janyo hankalin matan aure kan kayan mata, inda ya miƙa wasu daga cikin tsarabar da ya yi wa masu karatun mu tare da alƙawarin ci gaba a wani makon. To Allah mai komi da kowa ya ba mu ikon cikawa. Idan uwar gida shirya, sai mu ce asha karatu lafiya:
Nonon raƙumi idan ki ka haɗa shi da garin riɗi ki na sha zai ba ki fiye da tunanin ki a ni’ima. Sai dai fa yana buƙatar naci na ɗan lokaci kafin ya kama jikinki.
Ɓawan mangoro da ƙodagon za ki busar amma shanyar ɗaka, idan sun bushe, ki buɗe ki cire ƙwallon ki ƙara busar da shi, sai ki haɗe su ki dake, sai ki kwava su da zuma mai kyau ki yi matsi da shi na ɗan mintoci.
Ki samu ɗanyar bagaruwa ki ɗan soyata a wuta kaɗan, sai ki farfasa ta, ka da ki ki yi mata dakan da ruwan jikinta zai tsiyaye. Za ki ɗibi kaxɗan kiyi matsi da ita tsayin awa ɗaya, sai ki wanke da ruwa mai zafi, bayan kin wanke sai ki samu garwashi, ki zuba kuka da kanumfari kiyi tsuguni da shi.
Ɗanyar gyaɗa, alkama, aya, waken suya, minanas, gyeron tsuntsaye, garin zogale, ɓawan kankana(ba shanyar rana ba), za ki gyara kiyi gumba da su ki na damawa da madara ko nono marar tsami ki sha.
Ɗanyar gyaɗa za ki soya sama-sama, ki daka ta sosai, ki samu aya ita ma ki yi ma ta hakan, ki goge kwakwar ki bayan kin juye ruwan kin ajiye a gefe, ki samu garin mazanƙwaila, garin hulba(kaɗan). Uwar gida za ta haɗe su amma kwakwar a sanyata a ƙarshe tare da zuba ruwanta. Za ki sha da nono marar tsami. A sanya a firijin don gudun lalacewa.
Uwar gida ki samu habbatu sauda da kuma albabunaj ki dafa su tare da ruwa. Ki dinga sha tare da tsarki akai akai.
