Ta yi garkuwa da mijinta kan rashin kwanciyar aure

Manhaja logo

Wata matar aure da ta yi garkuwa da mijinta domin ta karɓi kuɗin fansa ta shiga hannun hukuma.

Dubun matar ta cika ne bayan ta karɓi kuɗin fansa Naira miliyan biyu bayan ta yi garkuwa da mijin nata.

Sai dai ta shaida wa ’yan sanda cewa, “Wanda ya yi garkuwa da shi ya karvi kuɗin fansa Naira miliyan biyu, amma bai ba ni kasona daga ciki ba, ko fasalin kuɗin ban gani ba.”

Ta bayyana cewa, ta sa an yi garkuwa da shi ne saboda rashin kwanciyar aure da ita da kuma watsi da ’ya’yansu.

Matar dai tana cikin mutum 29 da ’yan sanda suka gabatar wa ’yan jarida kan zargin garkuwa da mutane da sauran laifuka a Jihar Akwa Ibom.

A cewarta, sakamakon watsi da ita da mijin nata ya yi ta fara yin aikatau domin ciyar da kanta da ’ya’yansu bayan mijin ya auri wata mata.

Hakan ne, a cewarta ya tilasta ta kitsa sace shi domin ta samu kuɗin kula da kanta da ’ya’yanta daga hannunsa, amma ta yi rashin sa’a asirinsu ya tonu ba tare da an ba ta rabonta daga cikin kuɗin ba.

Magidancin da aka kuɓutar, ya ce, tun ranar 21 ga watan Yuli, 2022 aka yi garkuwa da shi a harabar gidansa.

Da ya ke jawabi, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Akwa Ibom, Olatoye Durosinmi, ya ce, rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen murƙushe ayyukan laifi a faɗin jihar.