Malamin Islamiyya ya bayyana kashe iyayensa da ya yi a matsayin jihadi

Wani matashi da ya rankwaɗa wa mahaifansa biyu taɓarya ya kashe su, ya yi ikirarin cewa Jihadi ne abin da ya aikata.

Shi dai wannan matashi ya shaida wa ’yan sanda cewa, ya yi amfani da taɓarya wajen kashe mahaifan nasa ne saboda izgili da su ke masa idan yana yin ibada.

A baya mun kawo rahoton wanann abin al’ajabi da matashin ya hallaka mahaifiyarsa Hauwa, mai shekara 60 da mahafinsa Ahmad Muhammad, mai shekara 70, wanda kuma shi ne Daggacin ƙauyen Zarada-Sabuwa a Ƙaramar Hukumar Gagarawa ta Jihar Jigawa.

Bai tsaya a iya kansu ba, domin sai da ya rankwaɗa wa kishiyar mahaifiyarsa mai shekara 50, Hakilima Ahmadu tavaryar da kuma wani makwabcinsu, Kailu Badugu, wanda dattijo ne mai shekara 65.


Tuni dai mahaifan nasa suka ce ga garinku nan, amma an sallamo kishiyar mahaifiyarsa daga asibiti, shi kuma makwabcin nasu har yanzu yana kwance rai a hannun Allah a asibiti.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya shaida wa menama labarai ta waya a ranar Asabar cewa, matashin da ya yi wannan aika-aikar, malamin makarantar Islamiyya ne.

DSP Lawan Shiisu Adam ya ƙara da cewa, wanda ake zargin ya shaida musu cewa yana cikin hayyacinsa ya yi wannan aikata-aika da ya kira jihadi, kuma ba ya nadama.

Wanda ake zargi da kashe iyayensa

“Malami ne a wata makarantar Islamiyya, hankalinsa lafiya ƙalau, ba ya ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, domin ko goro ba ya ci.

“A lokacin da ’yan sanda ke masa tambayoyi, sai ya riqa ce musu ai shi jihadi ya yi, jihadi ya yi, kuma shi a kan hanya madaidaiciya ya ke, su kuwa waɗanda ya kashe, ba mutane ba ne,” inji Shiisu.

Ya ce, matashin ya shaida musu cewa, iyayen nasa sukan ce mishi mahaukaci a duk lokacin da ya ke yin wani abu na addini.

“Wannan na daga cikin dalilansa da ya bayyana wa ’yan sanda cewa sun sa ya kashe iyayen nasa kuma ba ya da na sani, ya shirya fuskantar kowane irin hukunci,” a cewar jami’in.