JAMB ta ayyana ranar da za ta fara fitar da sakamakon UTME

Hukumar shirya jarrabawar neman gurbin karatu a makarantun gaba da sakandare (JAMB) ta ayyana ranar da za ta fara fitar da sakamakon jarrabawar UTME da aka rubuta kwanan nan.

Cikin sanarwar da ta fitar ranar Litinin, JAMB ta ce za ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME ranar Talata, 2 ga watan Mayu, 2023.

Sama da mutum miliyan 1.6 ne suka rubuta jarrabawar UTME a makon jiya don neman gurbin karatu a makarantun gaba da sakandare daban-daban da ke faɗin ƙasar nan.

Hukumar ta ce, ta amince ta fara fitar da sakamakon jarrabawar ne bayan taron gaggawar da ta gudanar a ranar Asabar.

Ta ƙara da cewa, ta yi jinkirin fitar da sakamakon ne don tabbatar da an kammala duk wani tantancewa.

Haka nan, ta sanar da waɗanda suka fuskanci ƙalubale yayin rubuta jarrabawar wanda ba su san da hakan ba cewar za su samu sanarwar lokacin da za su sake rubuta jarrabawarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *