NAFDAC ta haramta shigo da Indomie Nijeriya

Hukumar Kula da Inganci Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta ce an haramta shigo da taliyar Indomie zuwa Nijeriya daga ƙetare bayan da aka yi zargin gano sanadari mai haddasa cutar daji ko kansa a cikin wani nau’in taliyar.

Majiyarmu ta ce a baya-bayan nan jami’an kiwon lafiya a ƙasashen Malaysia da Taiwan sun gano taliyar Indomie samfurin “Sapecial Chicken” na ɗauke da sanadarin ‘ethylene oxide’ mai ƙarfin haifar da cutar kansa.

Bayanai sun ce ‘Ethylene oxide’ sanadari ne da akan yi amfani da shi wajen kashe ƙwayoyin cuta a jikin kayan aikin kiwon lafiya.

Ma’aikatar Lafiya ta Malaysia ta ce, daga cikin samfurin Indomie 36 da ta gudanar da bincike a kai tun a 2022, ta gano guda 11 na ɗauke da sanadarin ‘ethylene oxide’.

Tuni ƙasashen biyu suka haramta amfanin da samfurin Indomin da lamarin ya shafa a ƙasashensu.

Sa’ilin da take ƙarin haske kan batun, Shugabar NAFDAC, Mojisola Adeyeye, ta ce hukumar za ta soma bincike kan taliyar Indomie a faɗin ƙasa bayan da ta samu labarin matakin da hukumomin Taiwan da Malaysia suka ɗauka.

Adeyeye ta shaida wa manema labarai ranar Litinin a Abuja cewar, ranar Talata, 2 ga Mayu, hukumar za ta fara bincike a kan Indomin da ake zargin da kuma sauran nau’ukan da ake da su a ƙasar.

“Gobe, 2 ga Mayu, 2023, sashen kula da ingancin abinci na NAFDAC zai ɗauki samfurin taliyar Indomie daga masana’anta inda ake sarrafa su da kuma bayan an shigar da su kasuwa don gudanar da bincike,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa, samfurin indomin da lamarin ya shafa na daga cikin jerin kayayyakin da Gwamnatin Tarayya ta haramta shigo da su ƙasa, tare da cewa da ma ba shi da rijista.

Ta ce, da ma dai Gwamnati ta rigaya ta haramta shigo da samfurin Indomie ɗin da ake zargi shekaru da suka gabata.