Jamhuriyar Benin za ta cigaba da tsare Igboho a asibiti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan gwagwarmayar ƙabilar Yarbawa, Cif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho Oosha, ya sake samun ’yancinsa bayan da hukumomin jamhuriyar Benin suka sake shi, bayan ya shafe kimanin watanni takwas a gidan yari.

Babban Lauyan Igboho, Cif Yomi Alliyu SAN, ya tabbatar da hakan a ranar Litinin da yamma.

Alliyu ya bayyana a cikin saƙon cewa Sunday Igboho ya sake samun ’yancin ne amma da sharaɗi zama a asibiti domin a kula da lafiyarsa a cikin Cotonou.

Ya kuma bayyana cewa, sakin Igboho na cikin yarjejeniyar cewa kada ya bar cibiyar kiwon lafiya ko Cotonou saboda kan kowanne dalili.

Ya ƙara da cewa, an tabbatar da ’yancin kan sharaɗi ne tare da tsoma bakin wasu fitattun ’yan ƙabilar Yarbawa, Farfesa Wole Soyinka da Farfesa Banji Akintoye.

Ƙungiyar ’yan sandan ƙasa da ƙasa mai yaƙi da miyagun laifuka ta kama Igboho da ɗaya daga cikin matansa Ropo a filin jirgin sama na Cadjehoun da ke birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin a kan hanyarsu ta zuwa Jamus a ranar Litinin, 19 ga Yuli, 2021.

Ɗan ƙabilar Yarbawa na ƙoƙarin ganin ya tsere daga Nijeriya bayan wani samame da aka yi da zubar da jini da tsakar dare a gidansa na Ibadan da jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka yi.

Rundunar ’yan sandan sirri ta kai farmakin da tsakar dare ta yi sanadin mutuwar mutum guda, a daidai lokacin da aka kama wasu magoya bayan Igboho 12.

Alliyu ya bayyana a cikin saƙon cewa, “ina sanar da ku cewa an sako Cif Sunday Adeyemo daga gidan yari ga likitocinsa.

“Amma aakin sa yana ƙarƙashin yarjejeniyar cewa kada ya tafi ko ina,” inji Lauyan.