Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.
Tsohon shugaban ƙasa marigayi Umaru Musa Yar’adua na daga cikin waɗanda Jami’ar Al- Qalam da ke Katsina za ta karrama a bikin yaye ɗalibai karo na 16 a Jami’ar.
Mataimakin shugaban Jami’ar Farfesa Nasiru Musa Yawuri ya bayyana wa manema labarai haka a ofishin sa.
Yace Jami’ar za ta yaye ɗalibai 1,433 da suka kammala karatun su daga 2023 zuwa 2024.
Farfesa Yawuri ya ƙara da cewa a cikin su ɗalibai 22 suka sami takardar shaidar karatun digiri na ɗaya sai 218 da suka sami shaida ta biyu.
Ɗalibai 641 suka sami takardar shaidar ƙaramin digiri na biyu sai kuma ɗalibai 7 masu digirin PHD.
Mataimakin shugaban Jami’ar ya bayyana wasu bukukuwa da za ayi da suka haɗa da musabaƙar karatun Al Kur’ani .
Akwai kuma gabatar da ƙasida akan ” Yancin kasuwanci da gyaran haraji a Nijeriya – shin yanayin tattalin arziki yayi dai dai da tsare tsaren gwamnati”?. Farfesa Yawuri ya ce.
Bugu da ƙari kuma za a gabatar da gasan karatun Kur’ani wanda shugaban hukumar gudanarwa na jami’ar Alhaji Aminu Ɗantata ya ɗauki nauyi.
Sai kuma karrama fitattu yan asalin jihar da digirin girmamawa a cikin su akwai tsohon shugaban ƙasa marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua.
Da babban ɗan kasuwa Alhaji Ɗahiru Barau Mangal sai Alhaji Bilya Sanda (Khadimul Islam)da kuma marigayi Walin Daura Alhaji Sani Buhari.