Afrika ta Kudu ta sassauta dokokin biza ga ‘yan Nijeriya

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta sanar da sauƙaƙa tsarin neman biza ga ‘yan Najeriya masu sha’awar yawon shaƙatawa da kasuwanci, inda yanzu za su iya nema ba tare da miƙa fasfo ba. Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya bayyana hakan a ranar Talata yayin buɗe zaman taron haɗin gwiwa na Najeriya da Afirka ta Kudu karo na 11 (BNC) a birnin Cape Town, wanda Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya halarta.

A cewar wata sanarwa daga mai ba Shugaban Najeriya shawara Bayo Onanuga, Shugaba Ramaphosa ya ce an sauƙaƙa tsarin neman biza don ba da damar tafiye-tafiye ga masu sha’awar kasuwanci da yawon shaƙatawa daga Najeriya. Har ila yau, ya bayyana cewa masu cancanta za su iya samun biza mai izinin shigowa da fita har tsawon shekaru biyar ba tare da matsala ba.

“Mun samar da yanayi mai sauƙi ga ‘yan kasuwar Nijeriya don samun biza har tsawon shekaru biyar. Wannan wani mataki ne na ƙarfafa tafiye-tafiye da hada-hadar kasuwanci tsakanin ƙasashenmu,” in ji Ramaphosa. Ya kuma yi alƙawarin cire duk wata matsala da ke kawo cikas ga jari da zuba hannun jari tsakanin ƙasashen biyu, tare da tabbatar da ingantaccen haɗin gwiwa.

Ramaphosa ya jinjina wa matakan gyara da gwamnatin Nijeriya ke ɗauka don bunƙasa yanayin kasuwanci da tabbatar da kariya ga masu saka hannun jari, ciki har da ‘yan Afirka ta Kudu. Ya bayyana cewa gwamnatin sa na ci gaba da ƙoƙari wajen sauƙaƙa yanayin kasuwanci a Afirka ta Kudu, domin ‘yan kasuwa su samu damarmaki a fannonin tattalin arziki daban-daban.

A ƙarshe, Shugaban ya yi nuni da cewa ci gaban ƙasashen Afirka da kuma ƙalubale da ƙasashen Kudancin Duniya ke fuskanta za su kasance a gaba-gaba a ajandar taron G20. Ya kuma yi kira da a ƙara zuba jari tsakanin ƙasashen biyu, yana mai cewa akwai makoma mai kyau a dangantakar Nijeriya da Afirka ta Kudu.