Daga AISHA ASAS
Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA), ta nisanta kanta da wata tallar taron ƙasa da ƙasa da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda aka nuna cewa, fitaccen mawaƙi Dauda Kahuta Rarara zai halarta tare da wata cibiya mai suna Pleasant College of Advanced Studies.
A cewar wata sanarwa da Daraktan Sashen Watsa Labarai da Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Malam Nasiru M. Abdul, ya fitar a yau, jami’ar ba ta da wata masaniya, kuma ba ta amince da kowane irin haɗin gwiwa da wannan cibiya ko wani ɓangare don shirya wannan taro.
“Ba mu da hannu a wannan taron da ake tallatawa. Babu wani hadin gwiwa tsakaninmu da Pleasant College of Advanced Studies, ko wata cibiya da ta shafi wannan taro da ake kira na ƙasa da ƙasa,” inji sanarwar.
Hukumar ta jami’ar ta buƙaci jama’a, musamman ma’aikatan ilimi da masu ruwa da tsaki a harkar nazari da bincike, da su yi hattara da irin wannan talla, su kuma yi watsi da shi, domin jami’ar ba za ta ɗauki alhakin duk wani abin da zai biyo baya ba daga halartar taron.
Wannan sanarwar na zuwa ne kwana ɗaya kafin shi ma fitaccen malami kuma farfesa daga sashin nazarin aikin jarida da ke jami’ar Bayero a Kano, kuma tsohon shugaban jami’ar koyo daga gida (NOUN), wato farfesa Abdalla Uba Adamu ya bayyana bacin ransa kan yanda aka rubuta sunansa cikin manyan baƙi da zasu gabatar da jawabai a taron da jami’ar Dutsinma a Jihar Katsina ta shirya haɗin gwiwa da wata kwaleji a jihar domin nazartar waƙoƙin ftaccen mawaƙin siyasar Dauda Kahutu Rarara.
A jawaban da farfesa ya wallafa a shafinsa na Facebook, wanda farfesan da kansa ya tabbatar wa Manhaja rubutun nasa ne ya ce: “Sam babu wanda ya neme ni kan wannan batun, kuma ba ma a yi min maganar taron ba, kawai ganin sunana na yi cikin masu gabatar da jawabai ko ince manyan baƙi a taron.”
Farfesa Abdallah ya ƙara da cewa, “Rara ba dan siyasa ba ne, waƙe yake, sannan idan aka ce ina gudunmawa da ya bayar ga cigaban siyasa a Najeriya babu shi.”
Idan ka cire waƙoƙin siyasar da yake da salon da yake amafani dashi, Rara ba komai ba ne” don haka yake ganin ba daidai ba ne irin wannan taron.
Duk da irin gudunmawa, bibiya da kuma nazartar ayyukan ƙirƙira (creativity) da yake yi, hakan bazai ba wa wasu damar mayar da su karnukan farautar yan siyasa ba ko mawaƙansu ba, kamar yanda magoya ko masoyan mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ke neman yi da sunan wai nazartar waƙoƙin sa, duk da ana masa kirari da shatan zamani.”
Sanarwar wannan taron ta fito ne da safiyar jiya ta shafin mataimaki na musamman ga Dauda Kahutu Rarara kan harkar sadarwar zamani Rabi’u Garba Gaya.
