Magana za mu yi aure da Momoh tunanin masu kallo ne, inji Jaruma Mansurah
DAGA MUKHTAR YAKUBU
Kusan shekaru ashirin kenan da suka gabata rabon da su ga fuskar jaruma Mansurah Isah a cikin finafinan Hausa ta fito a matsayin Jaruma.
A tsawon shekarun nan duk da tana cikin harkar fim din a matsayin ta na matar jarumi Sani Musa Danja har suka samu arzikin haihuwar ‘ya’ya har guda huɗu kafin auren na su ya mutu a shekarun da suka gabata, bayan sun shafe sama da shekaru goma a matsayin ma’aurata.
A Lokacin da auren Mansurah Isah da Sani Musa Danja ya mutu jama’a da dama sun zuba ido su ga inda Mansurah Isah ta sa gaba tare da tambayar ko za ta ci gaba da harkar fim ko kuma za ya koma gidan aurenta?
Sai dai hakan ba ta samu ba a lokacin, kawai sai ta ci gaba da harkar ta ta kasuwanci da kuma tallafa wa mabukata a ƙarƙashin godauniyar ta Today lefe, daga ƙarshe ma dai sai kawai aka ji ta yi wuff da wani Bayerabe a can birnin Iko. Sai dai kash! Auren bai je ko’ina ba kamar yadda ta fito ta bayyana a watanni biyu da suka gabata cewar tun da ta yi auren ma ba su haɗu ba, sai daga baya da ta yi masa magana ya ce ya manta. To daga nan dai auren ya mutu.
A cikin watan Yunin da ya gabata ne Mansurah Isah ta fito da sabuwar alƙiblar ta inda ba zato ba tsammani kawai aka gan ta ta fito a wani sabon fim da ta ɗauki nauyin shiryawa, kuma ta fito a matsayin jarumar fim ɗin tare da Aminu Aliyu Sharif Momoh a matsayin miji da mata.
Hotunan da suka bazu a soshiyal midiya, sun tayar da ƙura tare da tambayar Momoh da Mansurah Isah aure za su yi ne?
Hakan ya sa jama’a suka yi ta tofa albarkacin bakin su, wasu na ganin sun dace da juna a matsayin ma’aurata, yayin da wasu suke cewa me jiya ta yi bare yau? Auren ta da Sani Musa Danja sun rabu wanda yake auren soyayya ne na saurayi da budurwa ina kuma ga wannan. Ko babu komai dai labarin fim ɗin ya tayar da kura.
Sabon fim ɗin dai mai suna Jodhafim ne da Mansurah Isah ta ɗauki nauyin shiryawa, kuma ita ce jarumar fim ɗin sannan ita ce mai bada umarni.
Fim ɗin ya din na da wata sabuwar alƙibla ta Mansurah Isah ta daban a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood, domin matakai uku da ta taka a cikin fim ɗin ya isa ya bai wa kowa mamaki.
Farko ita jarumar da ta ja fim ɗin duk da kasance ta dade ba ta yi aktin ba matsayin da ta taka a fim ɗin Jodha ya nuna har yanzu za ta iya jan zaren ta a cikin harkar fim, domin kuwa ta yi abubuwa na jaruma da ba kowacce jaruma za ta yi ba a cikin jaruman da ake da su a cikin Kannywood.
Haka nan kasancewar ta a matsayin furodusa nan ma ta yi abin da ya dace. Duk da cewa ta saba finafinai da dama a baya kamar ‘Akila’ ‘Fanan’ da kuma ‘Faliha and Falisha’ wannan fim ɗin na ‘Jodha’ ya nuna Mansurah Isah ƙwararriyar furodusa ce. Domin kuwa an samar da kayan aiki na musamman, kuma komai an yi shi a muhallin sa, don haka masu aikin ba su yi ƙorafi ba har aka gama aikin.
Wani sabon salo da kuma Mansurah Isah ta zo da shi a sannan fim ɗin da ta kasance mai bada umarni, wanda hakan wani sabon abu ne a Masana’antar Kannywood a ce mace ta fito a matsayin mai bada umarni, wannan ya sa ma a tarihin Masana’antar Kannywood da wuya ka ji an ce ga wata mace da ta shahara a fagen bada umarni. Amma dai ita Mansurah Isah ta gwada fasahar ta a fim ɗin ‘Jodha’ da ta kasance mace mai bada umarni.
A lokacin da muka tambaye ta ko me ya sa ta shirya fim din a daidai wannan lokacin?
Sai ta ce “To ni daman duk wani fim da ka ga na shirya za ka ga yana da alaƙa da abubuwan da suke faruwa a daidai wannan lokacin.
Yanzu idan ka ɗauki fim ɗin ‘Akila’ ya yi daidai da lokacin da aka yi shi, haka ma lokacin da na yi fim ɗin ‘Fanan’ na duba matsalar da take faruwa a lokacin wacce ta shafi matsalolin yara. To shi ma fim ɗin ‘Jodha’ abin da ya ke faruwa a wannan lokacin muka kalla muka samar da labari mai kyau don mu isar da saƙon da ya kamata na faɗakarwa ga al’umma, don haka wannan abu ba sabon abu ne ba a wajen mu , sai dai duk lokacin da za mu yi aikin mu kan yi ƙoƙarin samar da abubuwan da mutane za su gamsu da saƙon da muke son mu isar ga jama’a ba tare da ya gundure su ba.”
Dangane da fitowa a matsayin jaruma kuma da muka tambaye ta cewa ta yi,
“Gaskiya na zaɓi na fito a matsayin jaruma ne domin na samar da abin da nake so, sannan fim cin ya nuna mace da ta wuce shekaru talatin ne kuma sai na ga ina kan wannan matsayin. Sannan kuma a yanzu idan ka duba kusan duk wata jaruma da zan kira na saka ta sai ka ga tana da aikin da ba za ta bani lokacin da nake buƙata ba, saboda yanzu ana yin finafinai masu dogon zango idan jaruma ta tafi sai ta yi wata tana aiki. To ko da na saka idan tana cikin aikin aka kira ta za ta bari ta tafi wancan. Don haka sai na ga abin da ya fi mini sauƙi na tsaya na yi abina don na samar da abin da nake buƙata, kuma Alhamdulillah, aiki ya yi kyau mun samu abin da muke buƙata.”
A game da fitowar ta da Aminu Aliyu Sharif Momoh a matsayin miji da mata kuwa cewa ta yi”
Ai shi fim ana duba cancanta ne idan za a saka jarumi. Yanzu da aka saka shi saboda ya dace da fim ɗin ai ka ga duniya ta ɗauka duk ana ta magana, to wannan abin ake buƙata a fim a yi abin da ya dace komai a yi shi a muhallin sa, yadda masu kallo za su gamsu da abin da suka kalla. Amma magana a kan ko za mu yi aure ko wata magana ta daban ai duk tunanin masu kallo ne, mu dai a wajen mu harkar fim ce kuma ita muka yi.”
A yanzu dai jama’a sun zuba ido suna jiran lokacin fitowar fim ɗin, inda Mansurah Isah ta ce,
“Fitowar fim ɗin zai kasance nan ba da jimawa ba. Don a yanzu mun fara yin magana da ƙungiyoyi da kuma manyan kamfanoni na duniya da muke buƙatar mu haɗa gwiwa da su wajen samun damar nuna shi a duk manyan gidajen talbijin da kafafen yaɗa labarai da sinimu, ta yadda saƙon zai shiga a dukkan saƙo da lungu na duniya.
Fatan mu dai jama’a su ba mu goyon baya da haɗin kai domin ganin mun samu nasarar da muke buƙata.”
