Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) ta yi kira ga Majalisar Dattawan Nijeriya da ta kafa kotunan shari’a a dukkan jihohin Kudu maso Yamma ciki har da Jihar Edo a ci gaba da aiwatar da gyaran tsarin mulkin ƙasar.
Kungiyar ta ce, ana hana Musulmin yankin samun tsarin shari’ar Musulunci da ake da su a arewacin Nujeriya.
Kungiyar MURIC ta kuma yi kira da a ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar da babu aiki a faɗin ƙasar domin ba wa Musulmi damar gudanar da sallar Juma’a ba tare da shamaki ba.
Ta dage cewa tsarin ƙarshen mako na ranar Asabar-Lahadi na nuna fifikon Kiristoci kuma ba ya nuna bambancin addini a Nijeriya.
Bugu da ƙari, MURIC ta ba da shawarar amincewa da auren Musulunci a hukumance tare da shigar da sabuwar shekarar Musulunci a matsayin ranar hutu.
Majalisar Dattawan da ta samu wakilcin manyan jami’ai ta tabbatar wa ƙungiyar cewa za a yi la’akari da shawarwarinta yadda ya kamata.
