KACRAN ta buƙaci Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas ta inganta harkar kiwon dabbobi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Fulani Makiyaya a Nijeriya ta Kulen Allah (KACRAN) ta yi kira ga Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas da ta ci gaba da yin tsare-tsaren da take yi na ganin an inganta harkar kiwon dabbobi da kuma ɗabbaƙa cigaban yankin na Arewa maso Gabas.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar wanda ya samu sa hannun shugabanta, Khalil Moh’d Bello, KACRAN ta yaba wa hukumar ta NEDC bisa ƙoƙari wajen ganin an samu zaman lafiya da sake ginda al’ummomi da kuma taimakawa makiyaya, inda ya kwatanta hukumar a matsayin abin koyi.

“Hukumar raya yankin arewa maso gabas ta kawo cigaba sosai, ciki har da ƙoƙarinta na ganin shugabancin da za a shigar da kowa da kowa,” inji sanarwar ƙungiyar.

Har ila yau, KACRAN ta yaba wa haɗin gwiwar da hukumar ke yi da ƙananan hukumomi da kuma jami’an tsaro don dawo da zaman lafiya, wanda ta ce yana da matukar muhimmanci domin ɗorewar ci gaba a yankin.

“Muna kuma yaba wa NEDC kan rawa da take takawa wajen kai agaji a bala’o’i da ake samu, musamman ma iftila’in ambaliya a Maiduguri da kuma ƙoƙarinta wajen sake gyara makarantu da asibitoci da hanyoyi da kuma gadoji,” inji ƙungiyar. 

By ukarofi