Kada ka fake da kisan Hanifa ka tatsi masu makarantu – PDP ga Gwamna Ganduje

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Jam’iyyar PDP ta ja kunnen Gwamnatin jihar Kano akan kada ta yi amfani da wannan damar wajen karvar kuɗi a hannun makarantu masu zaman kansu na Jihar Kano.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kano, Alhaji Wada Sagagi ne ya bayyana haka, inda ya yaba wa hukumomin tsaro na ɗaukar matakin gaggawa a kan dukkanin  makarantan jihar na kwace lasisinsu, tun a ranar Talata da ta gabata.

Shugaban ma PDP ya yaba da kokarin da jami’an tsaro su ka yi na yin binciken gaggawa na kamawa tare da gurfanar  da wanda ya yi garkuwa da kuma kashe Hanifa Abubakar.

Wada Sagagi ya kara da cewa “a matsayinsu na yan jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kano mun bi sahun ƴan Nigeriya wajen yadda aka gaggauta gurfanar da wanda ake zargi a gaban Babbar Kotun majistiri a jihar domin cigaba da shari’ar marigayi ya Hanifa ba tare da vata lokaci ba.”

Dangane da gyara harkokin Ilimin makarantu masu zaman kansu kuwa jam’iyyar PDP ta shawarci gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ta bi tsarin da ya dace kamar yadda dokar da ta kafa hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ta jihar Kano ta tanada wacce ta tsara duk ayyukan makarantun da ba na gwamnati ba a jihar.

“Mun samu labarin gwamna Ganduje ya janye lasisin  dukkanin makarantu masu zaman kansu na jihar Kano tare da mutumtaka da kishin ƙasa don haka za mu ja kunnen Gwamnatin jihar Kano akan kada ta yi amfani da wannan damar wajen karɓar kudade a hannun mamallaka makarantun.”

Jam’iyyar ta lura cewa  akwai tsarin gudanar da dokar lura da makarantu masu zaman kansu da tsohon gwamna Sanata Kwankwaso ta samar.

Duk da muhimmancin sake fasalin bangaren Ilimi na makarantun da aka dade da shi, amma bai kamata gwamnati Kano ta dauki mataki don ya zama wata hanyar karbar kudade a wajen makarantu masu zaman kansu ba.

Sannan jam’iyyar ta mika sakon ta’aziya ga iyalan marigayiya Hanifa da mutanen Kano bisa wannan lamari da ya jefa mune cikin juyayi da alhini.