Kano, Jigawa, Katsina da Zamfara na iya kasa biyan cikakken albashi a 2025 – Rahoto

Daga MAHDI MUSA MIHAMMAD

Binciken kasafin 2025 na jihohin Arewa maso Yamma ya nuna cewa Kano, Zamfara, Jigawa ba za su iya biyan albashi gaba ɗaya ba idan har za a dogara da kuɗaɗen shigar da suke samu a kasafin kuɗin shekarar 2025.

Kamar yadda takardar da SolaceBase ta samu ya nuna, gwamnatin jihar Kano ta ware Naira Biliyan 85.8 a matsayin kuɗaɗen shiga na cikin gida.

A halin yanzu, kasafin kuɗin da aka ware na ma’aikata ya kai Naira Biliyan 150.9.

Jihar Zamfara ta samu kasafin kuɗin shiga na cikin gida na Naira biliyan 32.8. Sai dai kuma jihar na shirin kashe Naira biliyan 58.3 ga ma’aikata.

A ɗaya ɓangaren kuma jihar Jigawa tana shirin kashe wa ma’aikata naira biliyan 90.7 tare da kiyasin kuɗaɗen shiga da ake samu a cikin gida na naira biliyan 83.5.

Kasafin kuɗin shiga na cikin gida na jihar Katsina ya kai Naira biliyan 64.4 yayin da kuɗin da ake soma ware wa ma’aikata ya kai Naira biliyan 67.1.

Wannan yana nufin cewa jihar ba za ta iya biyan ma’aikata cikakken albashi ba idan har ta dogara da kuɗaɗen shiga na cikin gida kaɗai.

Binciken ya nuna cewa jihar Kaduna na shirin samar da kuɗaɗen shiga na cikin gida na Naira biliyan 112, yayin da ta yi kasafin kuɗin ma’aikata na Naira biliyan 83.9. Wannan yana nufin cewa jihar, idan ta cika burinta na samun kuɗaɗen shiga na cikin gida za ta iya biyan ma’aikata kuma ta haka za ta biya albashi na 2025.