Tinubu ya himmatu wajen inganta samar da abinci a Nijeriya – Tuggar

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, Ministan Harkokin Waje na Nijeriya, ya tabbatar wa manoma da makiyaya a Udobo da ke yankin Gamawa a Jihar Bauchi, ƙudirin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kare haƙƙin filaye tare da bunƙasa noma, don wadata abinci a faɗin Nijeriya.

A yayin wani taro a wani garin noma mai cike da tarihi, ya bayyana tsare-tsaren Shugaba Bola Tinubu na yaƙi da matsalar ƙarancin abinci ta hanyar ƙarfafawa yankunan karkara, noman zamani, da samar da ababen more rayuwa.

Tsakanin shekarun 1960-70, Udubo ta kasance cibiyar noma a Nijeriya. Sai dai kuma gwamnatin jihar ta yi watsi da al’ummar yankin tun shekaru da dama da suka gabata, yayin da ambaliyar ruwa da sauyin yanayi ke ci gaba da yin tasiri a rayuwarsu da kuma amfanin gonakinsu, har sai da gwamnatin tarayya ya kai musu tallafin gaggawa.

Ambasada Tuggar ya yaba da hazaƙar da al’ummar ke da shi, yana mai cewa, “Wannan ƙasa ta ciyar da al’umma da dama. Muna da burin farfaɗo da yankin ba tare da korar waɗanda suka aikatu da wurin ba.”

Tuggar ya yi cikakken bayani kan dabarun Shugaba Tinubu ga Udobo da makamantansu ta hanyar yin alƙawarin kare filayen manoma.

Ministan ya kuma ƙara da cewa, gwamnatin tarayya tare da tallafi daga hukumar kula da harkokin kimiyya da fasaha ta ƙasa (NASENI) za ta inganta samar da ruwan sha ta yankin fadama na Udobo da kuma ɓullo da na’urorin zamani masu inganci da za su taimaka wajen inganta noma da kuma ƙara yin tasiri ga rayuwar al’umma.

Ministan ya kuma yi cikakken bayani kan matakai daban-daban da ya zauka a matsayinsa na Ministan Harkokin Waje na taimaka wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar da ta gabata da ta lalata ɗkmbin al’umma a ƙananan hukumomin da suka haɗa da al’ummar Udubo.

Bayan mummunar ambaliyar ruwa, ECOWAS-da aka samu ta hanyar yunƙurin diflomasiyya na Tuggar-da hukumomin tarayya za su ba da tallafin kayayyakin more rayuwa.

Hajiya Aisha, ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin ta gode wa Ambasada Tuggar da bai yi watsi da su ba. Ta ce al’ummar jihar sun yi watsi da su shekaru da dama ba tare da wani kwakkwaran matakin da zai taimaka musu wajen yaƙar sauyin yanayi da ke ƙara ta’azzara ambaliya ba.

“Muna matuƙar godiya ga Tuggar saboda goyon bayan da yake bai wa al’ummarmu. Na tabbata takin da ya ba mu zai taimaka wa manoma da yawa a lokacin damina mai zuwa,” inji ta.