Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi.
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kaddamar da hukumar kula da jami’ar kimiyya da ƙere-ƙere ta Andullahi Fodio da ke Alieru, mallakin Jihar, yana mai imanin cewar wakilan hukumar na da hazaƙar maido da zaman lafiya a jami’ar da kuma ficen da tayi wurin karatu.
A lokacin bikin, a Birnin Kebbi, Gwamna Idris yana mai yaƙinin cewar, shugaban hukumar wanda tsohon mataimakin shugaban gudanarwa ne na jami’ar, Farfesa Muhammad Abubakar Ka’oje, zai jagoranci sauran wakilan hukumar su cimma burin da aka kafa wannan makarantar ta ilmi mai zurfi don shi.
Yayi bayanin cewar rikice-rikicen da suka addabi jami’ar ya tilasta ma gwamnatin Jihar Kebbi ta rusa tsohuwar hukumar kula da jami’ar sannan kuma ta sallami mataimakin shugaban jami’ar, (Vice Chancellor), da kuma mataimakansa guda biyu, (deputy Vice Chancellors).
Gwamna Nasir Idris ya ce bada ɓata lokaci ba, gwamnatinsa tayi nazarin lamarin, sannan kuma ta zaɓo mutane masu karamci ta naɗa su wakilan hukumar, sannan kuma ta naɗa sabon mataimakin shugaban jami’ar na gudanarwa, da nufin shata hanyar ci gaba wurin bada ilmi mai nagarta ga ɗalibai.
Yayi imanin cewar wakilan hukumar kula da jami’ar na yanzu, za su jajirce wurin shawo kan ko wane irin ƙalubale da jami’ar ke fuskanta, a kai ga nasara.
Kwamred Idris yayi sharhin cewar gwamnatinsa ta yi rawar-gani wurin kawo ƙarshen rikicin da jami’ar ta tsunduma a ciki, yana mai cewar wannan jami’ar tamu ce, wajibine mu kare mata darajar ta.
Gwamnan ya bada tabbacin bai wa hukumar kula da hukumar gudanarwa na jami’ar, dukkan goyon baya na san-barka da kayayyakin da ake buƙata domin a cimma nasarar karatu.
A jawabinsa na amincewa a madadin sauran wakilai, sabon shugaban hukumar gudanarwa, Farfesa Muhammad Abubakar Ka’oje, yayi alƙawarin gudanar da aikinsu kamar yadda aka shar’anta.
Ya buƙaci gwamnati ta wanzar da ba su goyon baya da shawarwari wurin sauke wannan nauyin da aka ɗora masu.
