Komai da ruwanka: Yadda na ke tauna taura biyu a Kannywood da Nollywood – Usman Uzee

Daga AMINA YUSUF ALI

Hausawa dai kan ce, wai taura biyu ba ta taunuwa lokaci guda a cikin baki. To, amma ba haka ba ne ga Jarumi furodusa wanda ya ke taka rawa a fina-finan Hausa na masana’antar Kannywood da kuma takwararta ta Kudancin Nijeriya, wato, Nollywood. Usman Uzee ɗan asalin Jihar Kwara ne, amma girman Jihar Kaduna ne.

Ya yi digirinsa kala biyu a ɓangaren fannin siyasa da kuma harshen Ingilishi a jami’o’in Abuja da kuma Jos. Sannan ya cigaba da karatunsa a Afirka ta Kudu. Ya shiga harkar fim a shekarar 2003 a matsayin mai kwalliya. Usman ya fito a matsayin jarumi, sannan ya shirya manyan fina-finai a masana’antar Kannywood da Nollywood.

Wasu daga cikin finafinansa da suka lashe gasar finafinai ta shekara su ne, Oga Abuja (2013) da Maja (2014). A wata tattaunawarsa da  jaridar ‘Guardian’, wacce Wakiliyar Blueprint Manhaja, AMINA YUSUF ALI ta fassara, ya bayyna irin faɗi-tashin a masana’antar fim tun daga shigowar sa a matsayin mai kwalliya zuwa yau. 

TAMBAYA: Ka shigo masana’antar Fim a matsayin mai kwalliya, ya aka yi kuma aka samu canjin yanayi ka zama yadda kake a yau?
UZEE: Al’amarin ya fara ne tun daga shekarar 2003. A lokacin na sha yin  tattaki tun daga Kaduna zuwa Legas domin halartar zacen ‘yan wasa (audition) Amma na kasa samun dacewa. Sai na dawo Kaduna na cigaba da karatuna. Watarana na je zaven ‘yan wasan kamar yadda na saba, sai Allah ya haxa ni da Daraktan Fim, Andy Amenechi wanda a lokacin yana cikin shahararru a harkar. Shi ya ban shawarar cewa, zan iya samun nasara a wasu fannoni na harkar fim ba tare da lallai sai na dinga bayyana a cikin fim ba. To wannan shi ne abinda ya ƙarfafa min gwiwa na fara harkar kwalliya a fina-finai. Saboda haka, sai na zama mai kwalliya mataimaki ga Gabriel Okoli Gabzini wanda a yanzu furodusa ne mazaunin ƙasar Jamus a halin yanzu. Inda na shafe tsahon shekaru biyu ina ɗaukar masa jaka ina biye da shi duk inda zai je aiki. A shekarar 2005 na samu damar samun darasi a kan fannin kwalliyar a garin Afirka ta Kudu.

Bayan dawowata sai na zama mai kwalliya wanda kowa yake rububin yin aiki da shi a masana’antar fim. Inda na shirya Fim ɗina mai suna, ‘London boy’ a shekarar 2008. Bayan na amshi kambun AMVCA na ma fi iya kwalliya a fina-finai sai na ɗora ɗambar zama furodusa. Shi ma na je na yi karatun sanin makamar aikin furodusa na tsawon shekaru 2. To bayan na dawo ne, na shirya Fim ɗina na farko.

Wanda a sanadiyyar haka ne na haɗu da Ali Nuhu. Wanda ya ba ni shawarar da shigo harkar fina-finan Kannywood. Inda na ɗauki shawararsa na shirya Fim ɗin Hausa mai suna,’Maja’. Wanda na gwamutsa taurarin Nollywood, Jim Ikye, Nkem Owoh tare da wasu jaruman Kannywood. Fim ɗin kuma ya lashe gasar fina-finai ta ‘City People Entertainment Awards’ a matsayin fim ɗin da ya fi kowanne a shekarar 2014. Daga nan ne kuma na ji ina buƙatar na fara taka rawa a matsayin tauraro. Don haka, na nemi shawarar furodusa, Rogers Ofime kuma ya ba ni ƙwarin gwiwa. Inda na fara bayyana a wani shiri na Oprah Winfrey na taurarin zamani. Kamar wasa kuma shirin ya shahara sosa a Arewacin Nijeriya. Wannan shi ne mafarin soma fitowa ta a fina-finai a matsayin tauraro. Inda na fara da Fim ɗin Voiceless a matsayin babban tauraro. 

Me za a iya cewa game da shekarun da ka ɗauka kana shan gwagwarmaya har ka kai ga inda ka kai a yau?
Gaskiya nasarar babba ce. Ni kaina zan iya cewa ta zo min a ba-zata. Sai dai kawai na yi hamdala ga Allah (SWT).

Wanne ƙalubale kake fuskanta wajen gwama ayyukan Kannywood da Nollywood a lokaci guda?
Da farko dai na samu matsaloli sosai. Sannan ‘yan adawa ta kowanne ɓangare suka dinga kawo min suka. Amma na yi biris na dage don na samu nasara. Shi ya sa a cikin kowanne Fim da na shirya ko na fito a matsayin jarumi, ba na manta mafarina, daga inda na fito. 

Yanzu wanne sabon fim za ka yi mana albishir da shi?
A halin yanzu kam akwai fina-finaina da yawa da na fito a ciki. waɗanda a halin yanzu  ake aiki a kansu. A yanzu haka ma akwai wani mai suna Conversations in Transit wanda Rogers Ofime ne ya shirya, kuma Robert Peters ya ba da umarni. Sannan akwai wani mai suna Farin Jini za ku gan shi a  talabijin ɗin ROK2. Ga su nan dai birjik suna nan tafe. Domin gabaɗaya shekarar nan ban zauna ba. Ina da fina-finai da dama a qasa waɗanda ba za ku so su wuce ku ba. 

Mene ne ma’anar ado da kwalliya a wajenka?
Ado da kwalliya shi ne bayyana ƙawa a cikin wani lokaci ko wani waje sannan a jikin suturarka, takalmi, yanayin rayuwarka, da kuma ƙyale-ƙyali. Kawai ni a wajena ado shi ne salo da tsarin rayuwa. 

Ya ya salon adonka ya ke?
Sassauƙa, maras shirgi.

Wanne abinci ka fi so?
Sakwara da miyar kuɓewa.

Waɗanne abubuwan sha’awa ka fi son aiwatarwa?
Ina son wasan ƙwallo, tafiye-tafiye, ƙwallon tebur da kuma ciye-ciye. 

Idan da kana da ikon canza wani abu a ƙasar nan, a halin yanzu me za na canza? 
Zan so a karɓe mulki a mayar da shi hannun matasa.