Mawaƙi Salisu Mariri zai angonce yau Juma’a

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Idan Allah ya kaimu ƙarfe 2:30 na wannan rana ta Juma’a, za a ɗaura auren mawaƙi, jarumi kuma furodusa a masana’antar Kannywwod, Salisu Nuhu Mariri, tare da amaryarsa, Maryam Muhammad, a unguwar Rigasa da ke garin Kaduna.

Kamar yadda katin gayyatar auren ya sanar, matashin jarumin yana gayyatar ‘yan uwa da abokai da kuma dukkan masoyansa zuwa wajen wannan ɗaurin auren, kuma ga duk wanda bai samu damar zuwa ba, sai ya taya su da addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya.

Shi dai Salisu Nuhu Mariri, yana cikin mawaƙan harkar fim sama da shekaru 15 da suka wuce. Kuma baya ga kasancewar sa mawaƙi, shi furodusa ne da ya shirya finafinai masu yawa, sannan kuma shi jarumi ne da ya fito a cikin finafinai masu yawa tsawon shekaru masu yawa.

Da fatan Allah ya sa a yi biki lafiya, Ya bayar da zaman lafiya a rayuwar auren nasu.