Kotu ta ƙi amincewa da tsawaita wa’adin shugabannin ƙananan hukumomi a Ribas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babbar Kotun Jihar Ribas da ke zamanta a Fatakwal ta bayyana tsawaita wa’adin shugabannin ƙananan hukumomin jihar na tsawon watanni shida da ’yan majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Martins Amaewhule suka bukata, wanda ya savawa Kundin Tsarin Mulkin ƙasar, kuma ba shi da wani tasiri.

’Yan majalisa 27 da ke sansanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Cif Nyesom Wike, a bana, sun kafa dokar da ta tsawaita wa’adin shugabannin ƙananan hukumomi na tsawon shekaru uku da watanni uku.
Sai dai a hukuncin da kotun ta yanke a ranar Talata, ta ce sabuwar dokar ta saba wa Kundin Tsarin Mulkin shekarar 1999 da sashe na 9 (1) na dokar jihar Ribas na shekarar 2018, wanda ya ƙayyade shekaru 3 ga shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli.

Kotun ta bayar da hukuncin cewa ƙarin wa’adin shugabannin ƙananan hukumomi da aka yi kwanan nan bai inganta ba a cikin shari’a mai lamba PHC/1320/CS/2024, ƙarar da Hon. Enyiada Cookey-Gam da 6 Ors da Gwamnan Jihar Ribas da Ors.

A cikin hukuncinsa, Hon. Justice D.G. Kio ya bayyana cewa dokar qananan hukumomi mai lamba 2 na shekarar 2024, wadda ta nemi tsawaita wa’adin shugabannin da watanni shida, ya ci karo da kundin tsarin mulkin 1999 da sashe na 9 (1) na dokar ƙananan hukumomin jihar Ribas mai lamba 5 na shekarar 2018.