Kotu ta ba da belin Emefiele

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta ba da belin dakataccen Geamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Godwin Emefiele kan kuɗi Naira miliyan 20 da shaida guda.

Mai Shari’a Nicholas Oweibo ne ya ba da belin bayan da lauyan Emefiele, Joseph Daudu (SAN) ya shigar da buƙatar belin ga kotun.

Alaƙalin ya yi watsi ƙorafin Gwamnatin Tarayya kan Emefiele saboda rashin kare ƙorafin nata da hujjoji.

Kazalika, Emefiele ya ƙi amincewa da tuhumar da ake yi masa kan aiakata laifuka biyu da suka haɗa da mallakar bindiga da alburusai ta harantacciyar hanya.

An ba da belin Emefiele ɗin yayin zaman da kotun ta yi a wannan Talatar.

Wannan na zuwa ne bayan da Emefiele ya shafe makonni tsare a hannun hukumar DSS.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *