Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kotu a Switzerland ta wanke tsohon shugaban FIFA Sepp Blatter da mataimakinsa Michael Platini kan zargin cin hanci.
Blatter, mai shekara 83, ya bai wa Platini wasu kuɗi da suka kai kimanin Swiss francs miliyan biyu, daidai da fan miliyan 1.5 a ranar 18 ga watan Junairun 2011, bayan mako biyu aka tura kuɗin zuwa asusun Platini daga asusun FIFA.
Dukkansu dai sun musanta aikata ba daidai ba, inda suka ce kuɗin da aka biya Platini kuɗi ne na wani aiki da ya yi wa FIFA.
Bayan bayyana a gaban a yau Juma’a, Blatter ya ce, “Na san ina da wasu kura-kurai, amma a wannan tuhuma, ina da gaskiya.”
An dakatar da Blatter mai shekara 86 da kuma Platini mai shekara 67, daga harkokin wasanni a 2015.
Blatter, wanda ya fara jagorantar Fifa tun daga 1998 tare da Platini ya ƙaryata zargin da ake yi musu. Blatter ya ce ya yi farin ciki da hukuncin da kotun ta yi inda ya ce wasu ne kawai ke musu bita da kulli.
Shekara 17 da Blatter ya kwashe yana shugabantar FIFA sun ƙare ne bayan zarginsa da badalar kuɗi a 2015, wanda ya janyo aka dakatar da shi na tsawon shekara shida daga shiga harkokin ƙwallon ƙafa.
Ya yi zargin ana yaɗa bayanan ƙarya a kansa kan wasu kuɗi da ya karɓa bayan dawowa daga gasar cin Kofin Duniya ta 2014.
Shi ma bayan wanke shi da Kotu ta yi, Platini ya nuna farin-cikinsa kan bayyanar gaskiya a kan tuhumar da ake musu. ”ina cike da farinciki, ina kuma mika godewa dukkan ‘yan uwa da abokan arziki, ganin gaskiya ta yi halinta bayan tsawon shekara bakwai ana ƙarya da kuma ɓata mana suna.”
Platini, wanda ɗan asalin ƙasar Faransa ne, ya kasance ɗan wasa da ya sami nasarori da dama a fagen tamaula, inda ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon duniya ta Ballon d’Or.
Platini ya kuma jagoranci Faransa wajen lashe kofin Turai a 1984 da kuma a Juventus a 1985.