
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da aiwatar da hukuncin Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ya umarci a soke rajistar Jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu guda huɗu.
A cikin taƙaitaccen hukunci da ta yanke, kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana matakin a matsayin “babban raini ga tsarin shari’a,” tana mai cewa alkalin kotun ya yi watsi da umarnin da kotun ɗaukaka ƙarar ta bayar tun da farko.
Sauran jam’iyyun da hukuncin ya shafa sune Action People’s Party (APP), Action Alliance (AA), Zenith Labour Party (ZLP) da Accord Party (AP).
Kotun ta ce, umarnin nata na dakatar da aiwatar da hukuncin zai cigaba da aiki har sai an kammala sauraron ƙarar ɗaukaka ƙarar da ke gabanta.
Wannan mataki na nufin kotun ta soke hukuncin na umartar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta soke rajistar jam’iyyun har zuwa lokacin da ji hukunci na gaba yayin ɗaukaka ƙara.
