Koya wa matasa sana’o’i zai ba su damar dogaro da kai – Wasila Aybo

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Mai kamfanin ‘Wasila Aybo General Enterprises’ ta bayyana cewa abinda ya ja hankalinta wajen koya wa matasa sana’o’i shine duba da halin da al’umma suke ciki musamman matasa na rashin abin yi.

Hajiya Wasila Shu’aibu Aybo ta bayyana hakan ne a taron yaye mutum 174 da aka koya wa sana’o’i ƙarƙashin tsarin Kwankwasiyya.

Ta qara da cewa yadda matasa suka zama zauna-gari-banza da yawan mace-macen aure da iyaye maza da ke mutuwa a bar mata da marayu shi ya sa suke koya musu sana’o’i su samu abin yi da za su kula da kan su da ‘ya’yansu.

Wasila ta ce su kuma matasa hakan zai taimaka su ɗauke kansu daga shiga shaye-shaye da zai iya kai su ga aikata munanan halaye, kamar ƙwacen waya da sauran laifuka.

Hajiya Wasila ta ce ta jingina da tsarin Kwankwasiyya ne wajen bada horon sana’o’i ga maza da mata saboda ta taso ta ga mahaifinta akan wannan ra’ayi don haka ta tabbatar da tafiyar Kwankwasiyya ita ce ke da manufar da take da ita a zuciyarta shi ya sa ta alaƙanta kanta da ita.

Ta ce yanzu haka waɗanda suka koyi sana’o’i da aka yaye su 174 da sun fito ne daga ƙananan hukumomi guda shida na ƙwaryar birnin Kano da suka haɗa da Gwale, Ungogo, Dala, Kumbotso, Birnin Kano da kuma Fagge.

Ta ƙara da cewa daga ciki maza 40 ne, sauran kuma mata ne. Sannan sun bada horon koyon sana’o’i ne domin janyo hankalin matasa su san tafiyar kwankwasiyya ta manufa ce na ƙoƙarin inganta rayuwarsu.

Hajiya Wasila Shu’aibu Aybo Qunchi ta ce ba ta da haufi Gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf za ta ɗora akan irin ayyukan da injiniya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya yi domin ta san akan tafarkin Madugu suke, kuma suna tayasu da addu’a da fatan alkhairi, wannan mulki Allah ya sa su shiga lafiya su gama ana mararinsu.

A jawabinsa a yayin taron ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Birnin Kano, Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi ya bayyana jin daɗin sa bisa tsarin horas da matasa da Hajiya Wasila take akan sana’o’i ya ce za su bada gudummuwa da yakamata don cigaba da bunƙasar shirin.

Taron ya samu halartar wasu daga masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar NNPP.