A daina fargaba mu na da wadataccen mai – NNPCL

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Yayin da aka fara dogayen layuka a gidajen mai a wasu sassa na Nijeriya bayan sanarwar cire tallafin mai da sabon Shugaban Ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ce zai yi, kamfanin mai na NNPCL, ya ce jama’a su daina fargaba domin akwai wadataccen mai a ƙasa.

Shugaban kamfanin, Malam Mele Kyari, ya shaida wa BBC cewa, akwai mai don haka babu wata matsala da ya ke gani za a iya fuskanta da ta shafi qarancin mai.

“Dama duk lokacin da aka samu irin wannan jawabi daga shugabanni, sai mutane su yi ta tururuwa suna zuwa gidajen mai suna siyan mai fiye da wanda suke buqata saboda suna tsoro kada a ƙara kuɗin man,” a cewar Kyari.

Ya ƙara da cewa bai ga abin tsoro ba domin akwai mai sosai a ƙasa.

Dangane da batun cire tallafin man kuwa, shugaban na NNPCL, ya ce da ma tallafin ya jima da zame wa NNPC matsala, domin kuɗin kamfanin ake ɗauka ana biyan tallafin.

Ya ce, “Abin da shugaban ƙasar ya yi ya zo daidai da dokar ƙasa, domin matakin hakan ya dace sosai.”

Shi ma shugaban hukumar da ke kula da tsare-tsare da sa ido a kan harkokin man fetur a Nijeriyar NMDPRA Malam Faruk Ahmed, ya ce za su tabbatar farashin man bai wuce kima ba.

Ya ce, “Matakin shugaban ƙasar ya yi daidai da doka, domin tun a bara ya kamata a cire tallafin man.”

Bayan rantsuwar kama aiki ne, sabon shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya sanar da cire tallafin man, yana cewa gwamnatinsa za ta karkata kuɗaɗen zuwa wasu ɓangarorin ci gaban ƙasa.

“Tallafin man fetur ya tafi,” inji shi. “Muna yaba wa tsohuwar gwamnati bisa ƙoƙarin janye tallafin man fetur a hankali, wanda yake ƙara wa mai ƙarfi ƙarfi fiye da talaka.”

Ya ƙara da cewa: “Ba zai yiwu tallafin ya ci gaba da laƙume kuɗaɗe ba yayin da muke ƙarancin kuɗi.

A madadin haka, za mu mayar da kuɗin wajen ayyukan raya ƙasa, da ilimi, da harkokin lafiya, da kuma ayyukan da za su kyautata rayuwar miliyoyin ‘yan ƙasa.”