Rundunar ’yan sandan Kano ta kama masu laifi 93 cikin mako guda

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da kama mutane 93 da ake zargi da laifuka daban-daban a cikin kasa da mako guda a jihar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Muhammed Usaini Gumel ne ya tabbatar da haka yayin ganawa da ’yan jaridu a ranar Laraba 31 ga watan Mayu.

Gumel ya ƙara da cewa, binciken farko ya tabbatar da zargin da ake yi akan waɗanda aka kaman.

Ya ce, daga cikin zarge-zargen da ake musu akwai kawo cikas da kuma ɗaukar nauyinsu da aka yi don su kawo tarnaƙi yayin bikin ƙaddamar da sabuwar gwamnati ta Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa.

Ya cigaba da cewa, an samu wasu daga cikin waɗanda ake zargin da muggan makamai a tare da su don aiwatar da laifukansu.

Ya ce, abin baƙin ciki da tashin hankali shi ne yadda suke a cikin maye don aiwatar da duk abin da suka yi niyya akan al’umma da suka haɗa da fashi da ƙwace da kuma kawo cikas a wurin taron.

A cewarsa, “Duk waɗanda mu ke zargin, za a gurfanar da su a gaban kotu akan abin da ake tuhumarsu.

“Ina da ƙwarin gwiwar cewa kotu za ta ɗauki matakin da ya dace akansu, don zama misali ga masu shirin aikata irin waɗannan laifuka.”