Sababbi da tsofaffin gwamnoni sun kai wa Buhari ziyarar ban-gajiya

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wata ƙasaitacciyar tawaga da ta ƙunshi gwamnoni masu ci da kuma tsofaffi, ta kai wa tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ziyarar ban-gajiya a mahaifarsa dake Daura ta Jihar Katsina a jiya Alhamis, 1 ga Yuni, 2023.

Daga cikin gwamnonin akwai sabon gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, Dapo Abiodun na Jihar Ogun, Babajide Sanwo Olu na Jihar Legas, Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, Bala Muhammad na Jihar Bauchi, Hope Uzodinma na Jihar Imo da mataimakin gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdulsalam.

A sanarwar da ofishin babban mataimaki na musamman akan kafafen yaɗa labarai na zamani ya fitar, ya bayyana cewa, sauran ’yan tawagar gwamnonin sun ƙunshi tsofaffin gwamnoni na Jihar Neja, Abubakar Sani Bello;  Jihar Jigawa, Abubakar Badaru; Jihar Kebbi, Atiku Bagudu; Jihar Filato, Simon Lalong da kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.