Sevilla ta lashe kofin Europa bayan doke Roma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sevilla ta doke Roma a bugun fenariti tare da lashe kofin Europa karo na 7 yayin wasansa ƙarshe cikin daren Laraba a filin wasa na Puskas Arena da ke Budapest.

Tun farko Dybala ya fara zurawa Roma ƙwallonta a minti na 34 da taimakon Mancini amma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Sevilla ta farke sakamakon kuskuren zura ƙwallon da Mancini ya yi a ragarsu, dalilin da ya sa kenan har aka kai ƙarshen wasa ana ƙwallo 1-1.

Bayan ƙarƙare hatta ƙarin lokacin da aka yi wa karawar ta jiya ne kuma aka tafi bugun fenariti wato daga kai sai mai tsaron raga, inda Sevilla ta zura ƙwallaye 4 cikin biyar da ta doka a ɓangare guda Roma ta iya zura ƙwallo 1 tare da barar da hudu.

Nasarar na nuna cewa ƙungiyar ta Spaniya zuwa yanzu ta lashe dukkanin wasannin ƙarshe 7 da ta doka a gasar tun bayan jagoranci Kyaftin Jesus Navas da ya kai su ga lashe kofin na farko a shekarar 2006 lokacin da suka doke Middlesbrough.

Wannan ne dai wasan ƙarshe na farko da Mourinho ya jagoranta ba tare da samun nasara ba, bayan kai Roma ga nasarar lashe kofin Europa Conference League a bara.