Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A makon da ya gabata akwai wani muhimmin batu da ya ɗauki hankalin jama’a a zaurukan sada zumunta dangane da batun wata matashiya ’yar gwagwarmaya Malama Layla Ali Othman wacce a wata hira da ta yi da wani shiri na tashar BBC Hausa ta bayyana halin da mata zawarawa ke fuskanta, tare da labarin irin halin da ita ma ta samu kanta a ciki bayan rabuwar aurenta da wasu mazaje.
Babu shakka jama’a da dama sun yi tsokaci iri-iri a kai, gwargwadon fahimtar da suka yi wa jawabin nata. Akasari martani masu zafi ya fi fitowa ne daga ɓangaren maza, yayin da a gefen mata da dama suka riƙa tausaya mata da nuna mata goyon baya. Mai yiwuwa ko don su sun fi fahimtar karatun nata ne, a matsayinsu na mata, tunda an ce ciwon ’ya mace na ’ya mace ne? Amma dai kam lallai Layla ta sha raddi sosai, kodayake a irin yadda na fahimce ta, ko a jikinta!
Sai dai kuma lokaci ya yi bayan an gama mayar da martani da raddi cikin fushi ko cikin raha, har da ’yan tamore, kar a ce su ma basu ce komai ba. Ya kamata kuma mu dawo mu yi karatun ta natsu, mu kalli al’amarin da idanun basira. Lallai ne duk ɗan halak ya so aure, saboda shi ne tushen mu, shi ne gatan mu, kuma shi ya martaba mu, ya mayar da mu masu kima da mutunci a idon duniya.
Don haka ne muka ji zafi da muka ji irin maganganun da ke fitowa na sukar aure, ba don mun damu mu tsoma baki a rayuwar Layla ba, sai don aure yana cikin ginshiƙin rayuwar mu. Dole ne mu fito mu kare mutuncinsa.
Sai dai kuma duk da haka, Hausawa na cewa, bayan tiya akwai wata caca! Bayan mun yi bambamin mun gama, ya kamata mu juyo mu kalli irin riqon da muke yi wa auren, musamman a nan Arewa, ko a tsakanin Musulmi.
Mu tambayi kan mu, shin muna bai wa auren muhimmancin da ya kamata? Muna kula da haƙƙoƙin auren da ke kan mu? Yaya muke riƙe amanar matan da muke aura, bayan mun raba su da iyayensu da dangin su? Shin muna kula da nauyin iyalinmu yadda malamai suka ce gwargwadon hali?
Amsoshin waɗannan tambayoyi su ne za su kai mu ga fahimtar abin da Layla ta tono, wato a Turance ake cewa, A CAN OF WORMS! Ban kawar da batun Yahudanci ko wayewar zamani na sa wasu matan Arewa tunanin rayuwarsu za ta fi kyau idan sun yar da ƙwallon mangwaro sun huta da ƙuda ba. Amma zance na gaskiya duk macen da ka ji ta fito bainar jama’a tana gayawa duniya ta haqura da aure a rayuwarta to, ka bincika da kyau ka gani. Ba a banza ba ne.
Ba lallai uzurin Layla na rabuwa da mazajenta biyu na aure ya samu karɓuwa a wajena ko kai ba, amma lallai mu duba a kusa da mu ba da nisa ba. Ba mu da ƙannai ko yayu mata, kai ko ma ’ya’ya, (tunda mu ma yanzu mun fara aurar da na ’yan uwa) ko wata mace a ’yan uwanmu ko a maƙwafta, waɗanda aure ya birkita rayuwarsu, suka fita hayyacinsu, wasu ma ciwon zuciya da hawan jini ya yi sanadin barin su duniya?
A dalilin halayen wasu mazan ne da ba su iya riƙon aure ba, ko ba su kula da riƙon amanar aure ba, haka take faruwa. Wani lokaci muna sane za mu rufe ido mu tilasta su komawa ɗakin mazajen su, ba don ba mu fahimci halin da suke ciki ba, sai don ba ma son su kashe auren su dawo gida zaman zawarci, ko ba ma son rayuwarsu ta ƙara shiga wani hali saboda rashin auren. Sai dai wani lokaci mu rarrashe su, ko mu tallafa musu da wani abu da za su rage zafi ko su kama sana’a a ɗakunansu na aure.
Kamar yadda muka tashi muka ji iyayenmu na faɗa ne, kuma masana zamantakewa suka tabbatar da haka. Aure ɗan haƙuri, kuma zo mu zauna ne zo mu saɓa. Ko da ma’auratan da za ka ji ana ce sun shafe tsawon shekaru suna zaune ba tare da sun rabu ko sun kashe auren su ba, idan ka yi bincike a tsanake za ka ji irin yadda suke ƙoƙarin fahimtar junansu da warware saɓanin da suke samu a sirrance ba tare da barin wani ya sani ba.
A haka kuma har suka laƙanci hikimar zama da juna, ba tare da wani ya ji kansu ba, kuma har ma ake tunanin ba sa faɗa da juna ko samun saɓani. Sirrin kamar yadda a cikinsu ke faɗa shi ne ɗaya ya mayar da kansa wawa, ka iya kawar da kai da kuma auna kanka da na abokin zamanka, musamman a game da batun haƙƙoƙi da mutunta juna.
Amma a yadda zamantakewar auratayya ta samu kai a wannan lokaci namu, abubuwa da dama ba sa tafiya daidai. Wasu gidajen zaman cutar da juna ake yi ba zaman haquri ko kyautatawa juna ba. Ko dai ka samu mijin azzalumi ne ya hana iyalinsa sakat, ba ya kyautata musu, babu magana mai daɗi, babu sauke haƙƙi, kuma babu ɗaga ƙafa. Ko da akwai wadatar za ka ga iyalin ba sa iya tantance akwai da babunsa, a waje ya yi sharholiyarsa amma a gida iyalinsa suna kokawa kan abin da za su ci.
Rayuwa a ƙuntace kamar zaman bauta ba zaman aure ba. Har matan mu na yi mana kallon mazan Arewa ba su iya nunawa mata soyayya, musamman matansu na aure. Sauƙin ta ma idan ana ɗokin ki a waje kafin a auro ki, ki shiga cikin gidan. Kamar abin da ake ce wa, fara’a daga waje, in ka shigo ciki ka zama nama. Kaico!
To, kuma ko mu ma mazan sau da dama haka muke gani. Soyayyar mu da mata a waje ne, amma da zarar an yi aure sai ka rantse da Allah canje aka yi maka, ba ita ce wannan mai yawan kwalliya da gyaran jiki, da fesa Turaren ba.
Ko ba ita ce mai tausasa kalamai da nuna kulawa da tausayawa ba, wacce ka ke tunanin da zarar kun yi aure ka gama samun farincikin duniya. Amma abin takaici ba za a fi ’yan makonni ko watanni da aurenku ba, sai ka nemi komai ka rasa, ka ji ko zama kusa da ita ƙyama yake ba ka, ballantana kuma batun kwanciyar aure. Sha’awar da a waje ku ke ji kamar ta kashe ku yanzu babu ita, kullum kuna ganin laifin juna.
Shi ya sa nake goyon bayan buƙatar da wasu masana harkokin zamantakewa da sasanta tsakanin ma’aurata suka gabatar na cewa a riƙa shiryawa matasan mu bita kan sanin haƙƙoƙin juna a matsayin ’yan Adam da kuma matsayin ma’aurata. Mene ne aure? Yaya ya kamata mu zauna da juna?
Yaya za mu riqa raya soyayyar da muka fara ginawa tun daga waje, da yadda za mu fahimci uzurorin juna a matsayin mu na mutane, da kuma yadda tarbiyyantar da kawunanmu da zuriyar da za mu haifa kan sanin martabar aure da zamantakewa tsakanin ma’aurata. Babu shakka hakan zai taimaka mana sosai wajen samar da iyali mai nagarta, da sanin ya kamata.
Kuskure ne a riƙa samun ‘ya’yan Musulmi kuma ’yan Arewa da ke ganin, aure ba alheri ba ne a wajen su, ko kuma babu wani namiji ko mace tagari da za a yi zaman aure na rufin asiri da mutumtaka da su. Duk yadda ki ka kai da jin zafi a ranki, don wani namiji ya yaudare ki, ya ci zarafinki, ko ya ci amanarki, da sauran su, ba hujja ba ce ta aibata aure gabaɗaya ko yi wa duk mazaje baƙin fenti ba.
Haka kai ma bawan Allah, ba duka mata ne abin gudu ba, lallai mata ni’ima ne kuma rahama ne ga duk wani ɗa namiji. Bai kamata mu riƙa ɗaukarsu a ƙasƙance, ko a wulaƙance muna muzguna musu ba. Mu sani fa ƙauna ce ta sa muka rabo su da gidajen iyayensu da ’yan uwansu, kada mu tozarta su ko mu yi watsi da yanayin su a yadda Allah Ya halicce su. Dole ne mu zauna tare da su cikin haquri da kyautatawa.
Lallai ya kamata mu sani Ubangiji zai tambaye mu kan amanar da ya ba mu haƙƙin kulawa. Mu tsaya mu kula da mutuncin iyalinmu, da na ’yan uwanmu mata. Mu tsare darajar aure. Kar mu riƙa tsangwama ko ƙyamar waɗanda wani dalili ya fitar da su daga gidajen su na aure. Mu kwaɗaitar musu aure yana da daɗi, kuma yin sa abu ne mai kyau, sannan akwai maza nagari da za su iya riƙe su da amana!