Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
ƙungiyoyin mata a ko ina a faɗin duniya, na gudanar da wani gangamin wayar da kan al’umma game da yaƙi da cin zarafin mata da tauye musu haƙƙoƙin su a fuskar shari’a, shugabanci, siyasa, da zamantakewa. Wannan gangami na tsawon kwanaki 16 wanda ake yi wa laƙabi da Orange the World a Turance, yana mayar da hankali ne wajen tattauna yadda za a kawo ƙarshen wasu matsaloli 16 da manyan mata da ƙananan yara mata ke fuskanta a cikin al’ummomi daban-daban na duniya.
Gangamin na so ne a kawo ƙarshen wulaƙanta mata a gidajen aure. A daina yi wa ƙananan yara mata aure da wuri ba tare da jikinsu ya ƙosa sosai ba. A daina yi wa yara mata kaciya. A daina wulaƙanta ko ƙasƙantasu su a zaurukan sada zumunta. A daina ƙyamatar mata masu ɗauke da cutar HIɓ da AIDS. A daina tauye haƙƙoƙin mata masu nakasa. A daina cutar da mata masu gudun hijira don tsira da rayuwarsu. A daina cin zarafin mata a wuraren ayyuka.
A daina cin zarafin ƙananan yara mata ana yi musu fyaɗe. A daina nuna ƙyama ga matan da suka fuskanci wani cin zarafi a rayuwarsu. A daina nuna wariya da ƙyama ga mata masu wasannin motsa jiki. A daina nunawa ’yan mata wariya a tsakanin matasa. A daina tursasawa mata yin jima’i ba da yardarsu ba. A daina tsangwamar mata masu neman jinsi ɗaya. A daina tauye haƙƙin mata na bayyana ra’ayoyinsu game da abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da shugabanci, a wuraren da suke zaune.
Ana fara wannan gangami na wayar da kai ne daga ranar 25 ga watan Nuwamba zuwa 10 ga watan Disamba na kowacce shekara. Mata da maza masu fafutukar kare haƙƙokin ɗan adam na haɗa hannu waje guda, domin nunawa duniya muhimmancin mata da maza su rayu tare cikin ’yanci da mutunta juna, ba tare da fuskantar wata wariya ko tsangwama ba.
Bincike ya nuna cewa an zaɓi ranar 25 ga watan Nuwamba ne domin ya dace da ranar da aka yi wasu mata da ake kira da ‘Mirabel Sisters’ kisan gilla a shekara ta 1941, sakamakon irin yadda suke sukar lamirin shugaban Jamhuriyar Dominica na wancan lokacin, abin da ya sa jami’an tsaro suka kashe su. Su waɗannan Mirabel Sisters sun kasance masu rajin kare haƙƙoƙin mata, da yaƙi da cin zarafi da ake wa mata a wancan lokacin.
A bana, gangamin kwanaki 16 na yaƙi da tauye haƙƙokin mata yana mayar da hankali ne ga buƙatar a waiwayi ƙudirin shekaru 30 na Babban Taron Mata na Duniya da aka gudanar a birnin Beijing waɗanne nasarori ko ƙalubale aka fuskanta? Wanne haɗin kai ko tallafi ƙungiyoyin mata da gwamnatoci ke buƙata don cimma nasarar waɗannan ƙudirori? Sannan harwayau, bikin yana ƙara mayar da hankali wajen kira ga masu faɗa a ji su zuba jari da nuna ƙwarin gwiwa ga yunƙurin kare martabar mata a ko ina. A riƙa nuna muhimmancin kula da lafiyar mata da ƙananan yara a ko ina.
Tsohon Babban Sakataren Majalisar ɗinkin Duniya Ban-Ki Moon ya taɓa ambatawa cewa, “Lallai ne a irin waɗannan kwanaki, gangamin ya mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a su daina yin shiru a duk inda suka ga ana wulaƙanta wata mace ko yarinya ƙarama, a tabbatar an ɗauki matakin dakatar da hakan.”
An fara ƙaddamar da wannan gangami ne a shekarar 2008 bisa lamuncewar Babban Sakataren Majalisar ɗinkin Duniya da wasu manyan ƙungiyoyin kare haƙƙokin mata na duniya, da nufin kafin nan da shekarar 2030 a kawo ƙarshen cin zarafin mata baki ɗaya a duniya. Wannan ya biyo bayan wasu ƙudirori ne da babban taron mata na duniya da aka gudanar a shekarar 1991 ƙarƙashin Cibiyar kula da Harkokin Mata Masu Faɗa A Ji ta Duniya, wato Women’s Global Leadership Initiatiɓe.
Tun daga sannan ƙungiyoyin duniya, da manyan ƙasashe ke ta rige-rigen sanya hannu cikin wannan gangami, inda aka ƙiyasta cewa zuwa shekarar 2013 an samu ƙasashe daban-daban har kimanin 63 da suka shiga cikin wannan gangami na kare martabar mata. Daga cikinsu an samu waɗanda suka kafa dokoki na kare haƙƙoƙin mata, samar da cibiyoyin nazarin yadda ake tauye haƙƙoƙi ko cin zarafin mata, gudanar da gangamin wayar da kan jama’a a kai-a kai, samar da tallafi ga matan da suka fuskanci cin zarafi da ƙuntatawa, da kuma samar da muhalli na musamman da za a riƙa ajiye matan da ake kora daga muhallansu ko suka gudu saboda yawan gallazawa da ake musu a wuraren da suke.
Masu rajin kare haƙƙoƙin mata na nuni da cewa, a cikin mata 4 da suke barin ƙasashen su don yin aikatau ko neman kuɗi, 3 daga cikinsu ana tilasta su shiga karuwanci ne ko amfani da su ta ƙarfin tsiya. Har wa yau, ana samar da tallafin sana’o’in dogaro da kai ga mata, da ɗaukar nauyin karatun yara mata, da koya musu hanyoyin kare kai a wuraren da suke fuskantar cin zarafi.
A nan Nijeriya, jihohin Arewa na daga cikin yankunan da ake zargin ba sa bai wa mata damar shiga a dama da su a harkokin shugabanci da siyasa, yayin da a ɓangaren al’adu da zamantakewa nan ma ake ganin a Arewa ne aka fi samun auren wuri da al’adar yi wa jarirai mata kaciya, da ma rashin bai wa yara mata damar yin karatu mai zurfi a makarantun boko. Don haka ake samun ƙarancin mata ’yan Arewa a wasu ɓangarori na ayyukan gwamnati, kamar harkar lafiya, tattalin arziki, siyasa da tsaro.
A wata ƙididdiga da aka fitar game da mata ’yan majalisu a Nijeriya, an gano cewa, jihohin Arewa irin su Borno da Yobe, Kano da Jigawa, Kaduna da Katsina, Bauci da Gombe, Sakkwato da Zamfara da Kebbi, Neja da Abuja, suna da ƙarancin mata ’yan siyasa da ke riƙe da kujerun majalisa. Haka kuma a Arewa ne aka fi samun mutuwar mata masu ciki da jarirai, saboda ƙarancin wayewa a kan harkar lafiya, da rashin bai wa zuwa awu da haihuwa a asibiti muhimmanci. Ga kuma wasu al’adu da ke hana wasu mazaje barin matansu suna zuwa asibiti.
A yayin da ake cigaba da wayar da kan jama’a game da muhimmancin mutunta haƙƙokin juna, ya kamata mu fahimci cewa, kowanne ɗan adam mace ko namiji na da ‘yancin yin rayuwa kamar kowa, yana da damar da zai riƙe ra’ayin kansa, ba tare da an nuna masa ƙyama ko wariya ba. Lallai ne mu kula da haƙƙoƙin iyalinmu, kare martabar matanmu da ’ya’yanmu mata. Mu basu kyakkyawar kulawa, da ’yancin samun duk abin da ɗa namiji yake da damar samu a matsayinsu na ‘yan’adam, musamman ilimi, lafiya, haƙƙoƙi, zarafi, uzuri, shawara, da sauransu.
Barista Mariya Shittu fitacciyar lauya ce mai kare haƙƙoƙin mata, kuma mamba a ƙungiyar Mata Lauyoyi ta FIDA reshen Jihar Filato, ta bayyana cewa, ‘Ya kamata masu wannan ra’ayi na musguna wa mata da ‘yammata su sani cewa duniya tana sane da wannan aika-aika da suke yi, kuma Allah da Hukuma ba za su ayale su ba.
Matuƙar ba a ɗaukar mataki kan masu mugun hali to, wasu ma za su riƙa ganin ba komai ba ne don su cutar da mace. Yin hakan ne kaɗai zai zama hanyar samun sauƙi ga mata. Sa’annan kuma raya waɗannan ranaku 16 da gangami na musamman zai wayarwa da mata kai su san cewa suna da haƙƙoƙi, kuma bai kamata a riƙa ci musu zarafi ba. Ya dace kuma a riƙa bibiyar lamarinsu, ana jin ra’ayoyinsu, da ɗaukar matakin share musu hawaye.
Babu shakka a matsayin mu na Musulmi ko Kirista, lallai idan muka yi riƙo da koyarwar addinanmu wajen kula da haƙƙoƙin abokan zamanmu, iyalinmu, da mawaftanmu, za a cimma nasara wajen cimma muradin Majalisar Dinkin Duniya na kawar da dukkan wata wariya, tauye haƙƙi, cin zarafi, ko ƙyama da ake nunawa mata a gidajensu na aure, wuraren ayyuka, makarantu, cikin anguwanninmu da lokutan yaƙi.