Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An yi kira ga matasan Jihar Kano da ma na ƙasa baki ɗaya da su ƙara himma wajen neman ilimi, na addinin Musulunci da na zamani, tare da koyon sana’o’in dogaro da kai.
Kwasau ɗin Sarkin Karaye, Ambasada Hashim Yahaya Jibrin Mijinyawa ne ya yi wannan kira yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Ambasada Hashim Yahaya Jibrin, wanda shi ne shugaban matasan ƙananan hukumomin Gwarzo, ƙaraye, Kabo, Rimin Gado, Bichi, Tsanyawa da Shanono, ya bayyana cewa rashin ilimi a tsakanin wasu matasa na taka rawa sosai wajen amfani da su wajen tayar da rikice-rikice a wasu sassan ƙasar nan.
Ya ce idan matasa suna da ilimi da kuma sana’o’i, ba za a iya amfani da su wajen haddasa tashin hankali ba, domin ilimi shi ne ginshiƙin al’umma mai nagarta.
Haka kuma, ya ja hankalin matasa da kada su bari wasu marasa kishin ƙasa su riƙa amfani da su wajen aikata abubuwan da ba su dace ba.
Ambasada Hashim Jibrin Mijinyawa ya kuma ƙara kira ga waɗanda suka kammala karatu da waɗanda ba su kammala ba da su rungumi sana’o’in dogaro da kai, maimakon jiran aikin gwamnati.
A ƙarshe, ya yi fatan alheri ga Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, da Sarkin Karaye, tare da addu’ar samun zaman lafiya da damina mai albarka ga al’ummar Musulmi da ƙasa baki ɗaya.
